Shi dai wannan zanen hoto wani fitaccen mai zanen barkwanci ne mai suna Mustapha Bulama ya zana shi. Bulama ya yi fice wajen zana hoton barkwanci domin nuna abinda ke faruwa a kasa batare da an yi maka bayani ba hoton ya ishe ka gane mai ake nufi.
Ganin cewa Ƴan Najeriya na fama da tsananin talauci da tsanannin tsadar abinci da wahalhalu na rashin tsaro ta ko-ina, kuma a haka dai iyalan shugaban kasa suka shirya kasaitaccen bukin ƴar su Hanan inda a wasu bidiyo aka rika nuna Ango da Amarya suna cashewa sannan an ta yi musu likin sabbin nairori, shi kuma mai zane ya zana wani hoto da ya bakanta wa uwargidan shugaban kasa rai.
Wannan zane dai ya nuna Aisha Buhari tsaye a gefen wani shirgegen rami tana rike da hoton gayyatar auren ƴarta da kuma hotunan su. A wannan zane dai an nuna Aisha na cewa ” Gashi nan dai, ko ba ku sami zuwa ba ku washe ido da hutunan bikin. Su kuma ƴan Najeriya na can Kasa cikin kududdufi suna ta gumi ruwa na neman ya tafi da su ita ko ta yake hakora.
BBC Hausa ta zanta da kakakin uwargidan shugaban kasa Aliyu Abdullahi, inda yayi mata bayanin bacin ran Aisha game da wannan zane na barkwanci da Bulama yayi.
Kamar yadda ya shaida wa BBC Hausa Aliyu ya ce “Zanen barkwancin Mustapha Bulama da ke yawo babu adalci a ciki saboda bikin ba shi da wata alaƙa da yanayin da yan kasa suka tsinci kansu, kuma saboda irin haka ne ya sa wata guda kafin bikin, shugabar tawa ta tattauna da ma’aikatanta cewa ba ta son a yayata bikin saboda za a taƙaita hidima.”
“Hoton da shugaba ta (Aisha Buhari) ta wallafa na ma’auratan a soshiyal midiya na bayan biki ne domin ta gode wa wadanda suka aike da fatan alheri da kuma sanar da ƴan kasa.
” Ina iya tabbatar muku cewa bikin Hanan Buhari shi ne wanda kwata-kwata babu armashi kuma aka taƙaita idan aka kwatanta da bukukuwan baya da aka yi a kasar nan.”
A karshe yayi karin haske game da Bidiyon da aka riƙa yadawa ana yi wa Amarya da Ango likin sabbin nairori su kuma sun gabza rawa.
“Wannan bidiyon da ke nuna mutane na liƙi da kudin naira ba a Abuja ba ne a gidan surukan Amarya ne bayan ta isa gidan dangin mijin a Kaduna,” a cewar kakakin uwargidan Buhari.
Ƴan Najeriya dai sun yi matukar fusata musamman a shafukan sada zumunta dake yanar gizo in da suka riƙa yin tir da wannan buki da kuma irin shagulgulan da aka yi a bikin. Wasu sun koka cewa a wannan hali da ake ciki a Najeriya na tsananin matsin rayuwa bai kamata a ce fadar shugaban kasa na yin irin wannan buki ba a wannan lokaci.