AREWA MASO YAMMA: Sojoji sun ƙara wa’adin yaƙi da ƴan bindiga har zuwa Disamba

0

Sojoin Najeriya sun bada sanarwar ƙara wa’adin ci gaba da fatattakar ƴan bindiga, masu garkuwa da mutane da ɓarayin shanu har zuwa watan Disamba.

Wannan yaki wanda suka sa wa suna ‘Operation Sahel Sanity’, ana gudanar da shi ne a Jihohin Arewa maso Yamma.

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai ne da kan sa ya bayyana haka, a lokacin da ya yi taron manema labarai a Sansanin Zaratan Sojoji na Musamman na 4 da ke Faskari, Jihar Katsina, a ranar Asabar.

Laftanar Janar Buratai ya ce bayan sun yi nazarin irin yakin da aka fafata, sun fahimci cewa akwai bukatar ci gaba da ragargazar sauran burbushin ‘yan bindigar da suka rage domin a kakkabe su gaba daya, yadda za a san an tabbatar da samun nasara mai dorewa baki daya.

Buratai ya ce an fadada wannan gagarimin yakin fatattakar mahara har zuwa yankin Arewa ta Tsakiya domin kara jaddada wanzar da zaman lafiya a kasar nan baki daya.

“Za mu ci karfafa hanyoyi da matakan bayanai.

“Duk da cewa zaratan sojojin mu na samun wahala wajen rashin sanin sirrikan lunguna, sako da surkukin dazuka a lokacin da suke arangama da ‘yan bindiga, a haka din ma sojojin su na samun galaba sosai.” Inji Buratai.

Daga nan ya yaba da irin goyon baya da hadin kan da sojoji ke samu a jihohin Zamfara da Katsina, musamman ta bangaren samun bayanan sirri.

Ya ce tilas mutanen cikin karkara su tashi tsaye haikan su na fallasa ‘yan bindiga da ke cikin su, cikin dangin su da abokan su.

Buratai ya yi gargadin cewa idan kuwa ba su yi hakan ba, to kan su ne suke cuta, domin wata rana wadannan ‘yan bindiga, a kan su makusantan na su za su juya da kai hare-hare.

Share.

game da Author