Jam’iyyar APC ta yi wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo raddi, bayan ragargazar da ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da salon mulkin sa.
Cikin wata sanarwa da Mataimakin Kakakin Yada Labarai na Kasa na APC, Yekini Nabena ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana Obasanjo a matsayin wani mutum mai bunu a jiki, wanda ba ya kai gudummawar kashe gobara.
Ya ce a lokacin gwamnatin Obasanjo ne duk wata lalacewa da rashawa da tafka rashin mutunci’ a gwamnati ya yi kamari.
“Ya kamata Obasanjo ya fito ya fada mana inda kudin wutar lantarki har dala bilyan 16 suke, wadanda gwamnatin sa ta ce ta kashe, amma ko fitilar-ruwa ba ta wadata kasar nan da su ba daga cikin kudaden.
“Shi da Mataimakin sa Atiku Abubakar sun sayar da wutar lantarki ga abokan su, abokan gwamnatin PDP.
Nabena ya ce yawancin matsalolin da suka dabaibaye Najeriya duk Obasanjo ne ya haddasa su.
“Shi ya kirkiro rudanin zabe na ko-a-ko-a-mutu, gwamnatin sa ta fara ayyuka masu dimbin yawa, ta tafi ta watsar da ayyukan, bayan an sace kudaden.
APC ta rika lissafo ayyukan da ta ce Shugaba Buhari ya yi wa kasar nan, duk kuwa da halin tabarbarewar da PDP ta gudu ta bar shi.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Obasanjo ya ce mulkin Buhari ya haddasa yunwa, kuncin rayuwa da rabuwar kan al’ummar Najeriya.
Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa fatara da yunwa, kuncin rayuwa da kuma rarrabuwar kawunan al’ummar kasar nan sun yi kamari a karkashin mulkin Buhari.
Obassnjo, wanda ya ce bai taba ganin an shiga mawuyacin halin da kasar nan ta shiga, kamar yanzu a karkashin mulkin Buhari ba, ya kara da cewa yanzu Najeriya ta zama hedikwatar talauci, yunwa da fatara ta duniya.
Ya ce ba wani abu ya janyo haka ba, sai makauniyar turbar tafiyar da mulki da jagorancin da wannan gwamnati ke yi wa kasar nan.
Obasanjo ya yi wannan kakkausan bayani a wani taro a Abuja, wanda mayan kungiyoyin da ke wakiltar yankuna, shiyyoyi da kabilu duk suka halarta.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Afenifere, Kungiyar Kare Muradin Yarabawa Zalla, sai Middle Belt Forum, Kungiyar Kare Muradin Kabilun Tsakiyar Najeriya.
Akwai kuma Kungiyar Dattawan Arewa, Kungiyar Ohanaeze Ndi Igbo, Kungiyar Kare Muradin Gurguzun Kabilar Igbo ds kuma Kungiyar Kare Muradin Yankin Neja Delta, wato Niger Delta Forum.
Yayin da Obasanjo ya yi kakakusan kiran cewa kada a kuskura a buga gangar yakin basasa ko yunkurin ballewa daga Najeriya, tsohon shugaban kasa din ya ce matsawar ana so Najeriya ta taka tudun-mun-tsira, to fa tilas sai an kasar da matsalar duk da ke haddasa kawu rarrabuwar kawuna tsakanin yanki da yanki, shiyya da shiyya ko kuma tsakanin wannan kabila da waccan.
“Na gamsu da yadda kowanen ku ke nuna damuwa da halin da aka jefa kasar nan, kamar yadda mu na muke nunawa.
“A yau Najeriya ta gaza a fannoni da dama, babu wani tasiri sai karin rarrabuwar kawuna da fatara da yunwa. Ta hanyar tattalin arziki kuwa, Najeriya ta zama cibiya da Hedikwatar yunwa, fatara da talauci ta duniya.
“Mu na ta ci gaba da taka tsani mu na hawa kololuwar lalacewa yadda kasashen duniya ke hango mu daga nesa a matsayin kasar da babu tsaro, kuma babu alamar sa.
“Kuma duk ba wani abu ne ya haddasa mana wannan jangwangwama ba, sai kwasar-,karan-mahaukaciya da wannan gwamnati ke yi wa tsarin shugabanci da jagoranci.”
Obassnjo ya yi kashedi ga masu fata ko mafarkin buga gangar yakin Basasa ko neman rabuwa ko ballewa daga Najeriya.
Ya nuna takaicin yadda Boko Haram, ‘yan bindiga, mahara da masu garkuwa da mutane ke ci gaba da yin kaka-gida a kasar nan.
Obasanjo ya kuma nuna takaicin yadda bashi ya cika ruwan cikin Najeriya tatil, har cikin na neman yin bindiga ya fashe.
Sai dai kuma Shugaban Buhari Media Organization, Niyi Akinsiju, ya ragargaji Obasanjo tare da nuna cewa ba laifin Buhari ba ne, laifin wasu manyan kasar nan ne masu amfani da kabilanci su na ruruta wuta.
Akinsiju ya ce masu bobbotai irin su Obasanjo, su na yi ne domin wannan gwamnati ta ki biya musu bukatun su na son ran su kawai.
Ya bayyana irin nasarori da kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi, bayan ya samu kasar marasa kishin kasa sun damalmala tattalin arzikin ta.
Ba Buhari Media Oganisation kadai suka maida wa Obasanjo martani ba, har da Fadar Shugaban Kasa da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed.