Gwamnatin Tarayya ta amince ta a kashe zunzurutun kuɗaɗe har dala bilyan 3.1 abin da ta kira, “zamanantar da aikin Hukumar Kwastan ta Najeriya.”
An cimma wannan matsaya ce a lokacin taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba, taron da aka gudanar a Fadar Shugaba Buhari.
Wannan gagarimin aiki dai za a ɗauki watanni 36 aka kashe kuɗaɗen kafin ya kammalu ko ya tabbata.
Zai karfafa dabaru da fasahar yin amfani na’urorin zamani wajen tafiyar da dukkan ayyukan da jami’an hana fasa-kwauri ke gudanarwa da kuma aiwatarwa.
“Maƙasudin wannan gagarimin aiki shi ne a ɗora ayyukan Hukumar Kwastan bisa turbar amfani da fasahar zamani, domin karfafa ayyukan hukumar, musamman a bangaren tara kudaden shiga.”
Haka Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ta bayyana wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, bayan kammala taron.
Ta ce an bayar da kwangilar aikin da za a kashe wadannan makudan kudade ga Messrs E. Customs HC Project Limited.
Ta ce kamfanonin zuba jari ne za su zuba kudaden, a bisa yarjejeniyar su riƙa kula da tara kuɗaɗe, su na kuma riƙa zame kuɗaɗen da suka kashe a cikin shekara 20.
Zainab ta ce idan aka kammala tsare-tsaren aikin, Hukumar Kwastan za ta iya tara dala bilyan 176 kafin kiftawa-da-bisimilla.
Minista Zainab ta ce muradin ta shi ne nan da shekaru kadan ta ga cewa manyan hanyoyin samun kudaden haraji da ba na fetur ba, sun zarce hada-hadar danyen mai da fetur samar wa Najeriya kuɗaɗen shiga.
Discussion about this post