Yayin da aka ki zaben dan takarar PDP Atiku Abubakar a zaben 2019, saboda ya ce zai sayar da kamfanin mai na NNPC, shekara daya da rabi bayan zabe Gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa za a nemi masu hannayen jari su sayi NNPC.
Karamin Ministan Harkokin Fetur Timipre Sylva ne ya bayyana cewa idan aka yi wa Kudirin Dokar Akbarkatun Man Fetur kwaskwarima, zai kasance babu wata dabara sai an saida kamfanin NNPC ga ‘yan kasuwa, amma ba ruguje shi za a yi ba.
Bukatar sayar da shi ta taso ne ganin yadda a yanzu gwamnati ta tsame hannun ta daga yanka farashin kudin litar fetur, an damka a hannun ‘yan kasuwa.
Dalilin haka ne aka nemi a gaggauta rusa Hukumar Rabawa da Sayar da Fetur da kuma yanka masa farashi, wato DPPRA.
Sylva ya bayyana labarin shirye-shiryen sayar da NNPC a hannun masu jari, a ranar Lahadi, ga manema labarai bayan ya fito daga taron da ya gana da Shugabannin Majalisar Dattawa da ta Tarayya.
“Mu na ta jin surutai barkatai game da NNPC wai za a rushe ta. To wannan dai ba ya cikin kudirin da mu ke so ya zama doka. Ba za a rushe NNPC, amma za a sahale ta ga ‘yan kasuwa domin su zuba jari, kamar yadda Gwamnati ke wa wadansu hukumomin ko kamfamonin ta.
Minista ya ce wannan tsari da aka shigo da shi zai amfani ‘yan yankin Neja Delta matuka fiye da yadda su ke amfana a yanzu.
PREMIUM TIMES ta bada rahoton yadda kudirin ya kunsa run kafin ya zama doka.
Dokar ta bijiro da cewa za a rushe Hukumar Yanka Wa Man Fetur Farashi (PPPRA). Sannan kuma maida kamfanin NNPC ya koma na ‘yan kasuwa, wato NNPC Limited.
Za a yi hakan ne bayan Ministan Harkokin Fetur da Ministar Harkokin Kudade sun kammala kididdige kadarorin NNPC kakaf.
A lokacin da ya gana da Shugabannin Majalisar Dattawa da na Tarayya, Sylva ya jaddada masu muhimmancin gaggauta amincewa da kudirin neman a sayar da NNPC, domin idan aka yi haka, Najeriya za ta bunkasa kuma za ta kasaita nan da shekarar 2040.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya sha alwashin cewa za su karya kwarin NNPC a wannan karo, ta hanyar sa wa Dokar Akbarkatun Man Fetur Hannu (PIB).
A na sa bayanin , Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ya ce za su amince da dokar, amma batun gaggawa ba shi ne alfanu ba. Mafi alfanu inji shi, abin da zai fi amfanar ‘yan Najeriya, idan gaggautawar ce, sai a gaggauta. Idan kuma jinkirtawa ce mafi alheri, to babu bukatar gaggawa.
Discussion about this post