An kashe ɗimbin ƴan Boko Haram a harin da sojoji su ka kai ta jiragen sama -Hedikwatar Tsaro

0

Ɓangaren Zaratan Kai Hari ta Sama na Sojojin ‘Operation Lafiya Dole’ sun karkashe Boko Haram masu yawa a wasu hare-hare daban-daban da aka kai wa sansanonin ƴan ta’addar.

Kodinatan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaro, John Enenche ne ya shaida haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce manyan nasarorin da aka samu sun hada da ragargaza sansanonin Boko Haram da ke Tongule, wanda aka yi a ranar 24 Ga Satumba, sai kuma wasu sansanonin a Bone da Isa a ranar 25 Ga Satumba.

Ya ce farmakin da aka wa Boko Haram a Tongule, ya faru ne bayan an yi amfani da tabaran-hangen-nesa an hango dandazon Boko Haram sun yi cincirindo a wurin da dare.

Ya ce an yi amfani da jiragen yaki a farmakin da aka kai a daidai inda su ka yi dandazon.

“A Bone kuwa, wani sansani ko matsuguni da ke hanyar Yale-Kumshe, shi ma sojojin sama ne su ka kai masa wannan harin da jiragen yaki da helikwaftoci. Sun kuma kashe da dama daga cikin Boko Haram din.

“Haka a Isari B Musa ma an gano
Boko Haram cikin dazuka kewaye da matsugunin su. Amma duk an karkashe su.”

Wasu Boko Haram Sun Yi Saranda’

Hedikwatar Tsaro ta ce akwai Boko Haram su 13 da su ka yi saranda tare da kananan yare 17 da matan aure shida, wadanda su ka yi saranda.

An ce sun yi saranda ne a kauyen Kodila a hannun Sojojin Bataliya ta 151 a Marabar Banki, cikin Karamar Hukumar Bama a Jihar Barno.

Share.

game da Author