An damke wani dauke da katin ATM 2,886 a filin jirgi, kan hanyar sa ta zuwa Dubai

0

Jami’an EFCC sun bayyana cewa su na binciken wani mutum da ake zargin dan damfara ne, bayan kama shi da aka yi da dumshen karin ATM a filin jirgin sama har guda 2,886.

An kama mutumin a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos, a lokacin da ya ke kokarin hawa jirgi zuwa Dubai.

Cikin wata sanarwa da Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya sa wa hannu a ranar Alhamis, ya ce wanda ake zargin mai suna Ishaq Abubakar, jami’an Kwastan na Najeriya ne suka damke shi a filin jirgin na Lagos.

Bayan sun kama shi ne suka damka shi a hannun EFCC a Shiyyar Ofishin EFCC da ke Lagos, domin a bincike shi, sannan a gurfanar da shi.

EFCC ta ruwaito Mataimakin Kwanturola na Kwastan Abdulmumini Bako ya na cewa, wanda ake zargin daga Kano ya isa filin jirgin, a kan hanyar sa ta hawa jirgi daga Lagos zuwa Dubai.

Ya ce wanda ake zargin ya yi niyyar fita zuwa Dubai ne ta jirgin Emirate, an gan shi tare da wani hadimin da ya rika kai da kawo a filin jirgin domin ganin cewa mutumin ya samu tsallakewa ya hau jirgi.

” Mutumin ya bode katin ATM din a cikin kwalayen Indomie. Wannan ne ya sa aka tilasta cewa sai an yi masa binciken-kwakwaf.”

Jami’in EFCC da ya karbi wanda ake zargin, ya ce za a yi bincike, kuma ya tabbatar da cewa za a gurfanar da duk wanda aka kama ya na da hannu a cikin wannan harkallar.

Ya ce EFCC zargin harkalla ce ta karkatar da kudade tsakanin wasu mutane da kuma ma’aikatan banki.

Ya kara da cewa sun lura kwanan nan ana yawan bude asusun ajiya a banki barkatar, ba tare da bankuna na tantance wadanda suka bude asusun an san su ido-da-ido ba.

Share.

game da Author