Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, ta raba kayan agaji ga wadanda ibtila’in ambaliya ta shafa a Jihar Kogi.
Aisha Buhari ta aika da kayan agaji masu tarin yawa domin rabawa a karkashin Kungiyar Future Assured, kamar yadda kakakin ta Aliyu Abdullahi ya bayyana.
Tawagar wadda ke karkashin Mai Baiwa Shugaba Buhari Shawara a Al’amurran Cikin Gida da Shirya Taruka, Zainab Kassim ta jagoranta, ta kai ziyarar gani da ido da kuma raba kayayyaki a Karamar Hukumar Koton Karfe da wasu unguwanni a Lokaja, inda rusa ya shafe gidajen unguwannin.
Cikin makon da ya gabata an nuno Ministar Harkokin Agaji da Jinkai, Sadiya Farouq ta na kewayen unguwannin da ruwan ya shafe a jirgin sama.
Uwsrgidan Gwamnan Kogi, Aisha Bello ce ta karbi kayayyakin a madadin wadanda ambaliyar ta shafa. Kuma ta yi kira da su yi amfani da kayan yadda ya dace.
Daga cikin abin da Aisha Buhari ta aika domin rabawa, har da shinkafa, wasu nau’ukan kayan abinci, sabulu, omo da kayan tsaftace-tsaftace, barguna da tufafi.
Tawagar ta karasa Asibitin Kwararru na Jihar Kogi, inda ta bayar da gudummawar kayan asibiti domin amfani a asibitin da kuma rabawa a Kananan Asibitocin Jihar.
Kayayyakin sun hada da kayan tsaftace-tsaftace, takunkumin baki da fuska, ruwan wanke hannaye, safar hannu domin amfanin likitoci da jami’an asibiti a lokacin tiyata.
Sannan kuma sun rika bi dakuna su na jajanta wa marasa lafiya.
Babban Daraktan Asibitin, Isa Shu’aibu ne ya karbi kayayyakin a madadin Hukumar Asibitin.
Shi ma Shugaban Kungiyar Manoman Kogi, Mohammed Sulaiman, ya gode wa Aisha Buhari, bisa ga gagarimin kayan agajin da ta aika wa Jihar Kogi.