AMBALIYAR JIGAWA: Mutum 40 sun mutu, Gonakin shinkafa, Masara, sun salwanta

0

Akalla mutum 40 ne suka rasu, sannan gonakin shinkafa, Masara masu dimbin yawa sun salwanta a a ambaliyar ruwa da ba a taba yin sa ba a tsawon shekaru 36 da suka wuce a jihar Kano Jigawa.

Mahukunta sun ce rayukan mutanen da aka rasa sun fito ne daga kananan hukumomi 19 da suka hada da Buji, Hadejia, Ringim, Taura, Jahun, Miga, Malammadori, Auyo, Kafinhausa, Guri, Gwaram, Kiyawa, Kaugama, Birnin- kudu, kirikasamma, Garki da Babura.

Sani Yusuf na hukumar SEMA ya ce karamar hukumar Hadejia ne ta fi afkawa cikin wannan ibtila’In.

Mahukunta sun ce, an samu ɓarkewar ruwa ne bayan dam dam ruwa na Tiga da Chalawa sun cika sun batse, sannan kuma da canjin yanayi da ake fama da shi.

Baya ga haka wasu sun koka cewa da kuma sakacin gwamnati na kin daukar mataki tunda wuri akai.

Sai sai kuma duk da tallafi da gwamnati ke cewa ta aika wa mutanen da wannan ibtila’I ya afkawa, wasu da yawa cikin mazaunan sun ce gwamnati ba yi musu abin azo a gani ba wajen aika musu da tallafi.

Akalla sama da Heta 100 na gonar shinkafa ne ya salwanta a sanadiyyar wannan ambaliya.

Mutane da dama sun rasa muhalli da dukiyoyin su.

Tabbas wannan ambalya zai kawo matsalar karancin abinci a kasa ganin wadannan yankunane gwamnati ta narka kudade domin tallafin ayyukan noma a bana, musamman manoman shinkafa.

Share.

game da Author