AMBALIYA: Manoman Kebbi sun yi asarar amfanin gona na sama da naira bilyan 5

0

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kebbi (SEMA), ta bayyana cewa ambaliya ta janyo wa manoman jihar asarar amfanin gona na sama da naira bilyan 5.

Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kebbi, Sani Dododo ne ya tabbatar da haka, a hirar sa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

A tattaunawar ta ranar Laraba, Dododo wadda aka yi da shi bayan ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu sanadiyyar hatsarin jirgin ruwa a Karamar Hukumar Jega, inda aka rasa rayukan mutum takwas.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta tallafa wa jihar domin saukaka wa wadanda suka yi dimbin asara.

Ya ce har yanzu ambaliyar ba ta gama yi wa jama’a ta’adi a gonakin su ba. Sannan kuma ta kashe mutane da dama.

“Ina kira ta kafafen yada labarai ga Gwamatin Tarayya da Kungiyoyin Bada Agaji na Kasa da Kasa to gaggauta kawo agajin gaggawa ga Gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar.

“Idan su ka taimaka, za mu fawwala mu hakura mu jira zuwan noman rani, domin mu rage asarar da ambaliya ta yi mana yanzu da damina.

“Tantancewa farko ta nuna an yi asarar shinkafa da sauran amfanin gona akalla na naira bilyan 5. Kuma ba a gama kididdigar yawan asarar da aka yi ba.

“Dama Hukumar Kula Da Yanayi ta Kasa ta ce a cikin Satumba za a yi ambaliya a kananan hukumomi 102. Cikin su kuwa 11 daga jihar Kebbi suke.”

Dododo ya ce ruwa ya mamaye sama da hekta 450,000 ta shinkafa. Ga kuma sama sama da hekta 50,000 ta gero, dawa, masara da rake wadanda ambaliya ta lalata.

“Idan ka hada zai ba ka hekta 500,000 kenan da ambaliya ta lalata.”

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa manoman jihar Kebbi bisa ga wannan mummunar barnar amfanin gona da ambaliya ta yi musu.

Share.

game da Author