Abin da ya sa ayyukan da Buhari ke yi su ka bambanta da alkawurran sa na lokacin kamfen -Fadar Shugaban Kasa

0

Ayyuka da ajandojin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a yanzu sun bambanta da alkawurran lokacin zabe. Kakakin Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasa ta fitar a ranar Litinin.

Shehu ya ce abubuwa mafi muhimmanci da gwamnati ta sa gaba, wadanda suka bambanta da alkawarin da aka yi a lokacin kamfen, sun dogara ne ga irin karfi da nauyin da aljihun gwamnati ke da shi.

Ya ce ita gwamnati aba mai tafiya ta na cin karo da muhimman abubuwa sosai. Don haka babu wata gwamnatin da za ta hau mulki har wa’adi biyu, kuma ta tsaya kawai a kan alkawurran da ta yi wa jama’a, kafin ta hau mulki.

Buhari ya kayar da shugaban lokacin, Goodluck Jonathan a zaben 2015. Ya sake yin nasara a zaben 2019.

Ya hau mulki tare da yin alkawarin samar da tsaro, hana cin rashawa da kuma inganta tattalin arziki.

Da ya ke wa jakadun kasashe bayani a cikin makon da ya gabata, Buhari ya shaida musu wasu ajandoji 9 da ya ce zai fi maida kai kafin karshen wa’adin sa. Sun hada da ilmi, yaki da rashawa, bunkasa noma, tattalin arziki, harkokin kiwon lafiya da inganta tsaro.

Garba ya ce Buhari ya bijiro da wasu ajandoji ne a daidai saura shekarun da suka rage masa a mulki.

Ya ce irin binciken da gwamnatin Buhari ke wa Hukumar EFCC ya kara tabbatar wa jama’a cewa da gaske ya na son ganin an dakile rashawa a kasar nan.

Ya ce za a ci gaba da yaki da Boko Haram, har sai an ga bayan su, sun zama tarihi.

A karshe ya ce tawayar da tattalin arziki ya samu a Najeriya da duniya baki daya saboda annobar Korona, ya na bukatar jajircewa wajen ganin an maida shi a kan sahihiyar hanya, ta hanyar bijiro da tsare-tsaren inganta tattalin arziki.

Share.

game da Author