Matashin mawaki Laycon, da ya fafata da wasu fitattun matasan Najeriya maza da mata ya lashe gasar ‘Big Brother’ da aka kammala yau a Legas.
Laycon na daga cikin wadanda ba a taba tsammanin zai lashe gasar ba, kamar yadda ake ganin da yawa daga cikin wadanda yake fafatawa da su na kawo wuta a gasar.
Hakan bai sa ya dimauce ba ko kuma ya tsorata ba. Abu dai kamar da wasa sai gashi ya fito cikin mutum biyar da zasu iya lashe gasar.
A ranar karshe aka cire Nengi, Leo da Vee.
Kafin ranar karshe, Laycon ya ci naira miliyan 6 a gasar da aka rika yi a wannan gida na ‘Big Brother’
Kyatar da Laycon ya samu
1 – Kudi Naira Milyan 30
2 – kerarrar Gida
3 – Mota kirar Jeep
4 – Kayan gida, Talbijin, Naurar sanyaya daki, da Firji.
5 – Lemon Pepsi da Indomie na shekara Daya.
6 – Za i tafi hutu Dublin, Dubai sannan ya kalli wasan karshe Champions League.