Ƴan Najeriya sun yi kira ga Atiku ya fito ya ja zugar zanga-zangar ƙarin ƙudin wutar lantarki

0

Ƴan Najeriya sun ce sun gaji da yadda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ke labewa a cikin soshiyal midiya ya na maida raddin adawa ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Sun ce idan dai da gaske neman zama shugaban kasa ya ke yi, to ya fito ya ja zugar zanga-zangar rashin amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki, su kuma za su fito, fitar farin-dango su mara masa baya.

Wannan raddi da aka yi wa Atiku ya zo ne jim kaɗan bayan ya wallafa sanarwar yin tir da karin kudin wutar lantarki a shafin sa na Twitter.

Atiku ya ce rashin tunani ne a ƙara kuɗin wutar lantarki, a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kwance su na jiyyar ciwon da kuncin rayuwa da suka shiga sakamakon karyewar tattalin arzikin Najeriya saboda fantsamar cutar Korona.

Sai dai kuma Jim kaɗan da fitar da wannan sanarwar ta Atiku a Twitter, ɗimbin ƴan Najeriya sun rika shiga shafin sa na Twitter din su na yin sukuwa da zamiyar-zakara da yi masa raga-raga’ a cikin kalamai na nuna masa goyon baya.

Ko Ka Fito Mu Yi Zanga-zanga Ko Ka Yi Shiru -‘Yan Najeriya ga Atiku

Atiku ya sha rubdugun kiraye-kirayen cewa ya kamata ya daina adawa a soshiyal midiya kadai. Ya fito ya ja zugar zanga-zanga ya ga yadda za su mara masa baya.

“Haba Atiku, kai kullum adawa a Twitter! Idan za ka fito a kan titi, kamar yadda Buhari ya fito ya yi wa Jonathan zanga-zanga a 2014, to kai ma ka fito.” Inji wani mai suna Bobby.

“In dai za ka ci gaba da labewa a Twitter da Facebook ka na adawa, to har abada ba za ka zama shugaban kasa ba. Ka fito kawai idan za ka fito kan titi. Mu kuma za mu take maka baya.” -Cewar Kabiru Usman.

“Don ka shiga shafin Twitter ka yi wa karin kudin wutar lantarki tir, wannan duk shirme ne. Atiku, idan za ka fito kan titi, ka fito kawai. Ba a bori da sanyin jiki. ‘Yan Najeriya na cikin wahala.” Inji wani mai suna Azeez Ola.

“APC da Buhari sun yi wa Jonathan zanga-zanga cikin 2014. Shin kai Atiku me ka ke shakka ne da ba za ka fito ka yi wa Buhari zanga-zanga a 2020 ba? Ka fito mu bi ka, mu da kai duk mu Sha barkonon-tsohuwa. Ka ga mu da kai kowa zai san da gaske kowa ke yi.” Inji Akunola Ajeku.

“Ba zanga-zanga za ta fito a yi kadai ba. Ka fito, mu fito duk mu tsaida komai a kasar nan, a tsaya cak!’ Inji King Cedar.

Dimbin mutane na ta ci gaba da bayyana ire-iren wadannan kakkausan kalaman kara wa Atiku kwarin-guiwa.

Atiku ya yi tir da karin wutar lantarki

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa babban rashin tunani ne gwamnatin tarayya ta yi wajen yin karin kudin wutar lantarki.

A wani kakkausan bayani da ya wallafa a shafin sa na Twitter, Atiku ya ce ba daidai ba ne a kara kudin wutar lantarki a daidai lokacin da jama’a ba su ma fara farfadowa daga dukan tsiya da kuncin rayuwa ya yi musu a lokacin Korona ba.

Ya ce an yi gaggawa wajen yin karin a lokacin da kayan abinci ke ci gaba da kara tsawwala tsada. An kuma kara kudin fetur duk a wannan lokaci.

Share.

game da Author