Ƴan Najeriya ke ja wa kan su wulaƙanci da cin mutunci a China, Afrika ta Kudu da wasu kasashe – Aminu Wali

0

Tsohon Sakataren Dindindin na Majalisar Dinkin Duniya, kuma tsohon Jakadan Najeriya a China, Aminu Wali, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ne da kan su ke jawo ana wulakanta su da cin mutuncin su musamman a China, Afrika ta Kudu da wasu daidaikun kasashe.

A tattaunawa ta musamman da Wali ya yi da PREMIUM TIMES, ya bayyana irin jekala-jekalar da ya rika fama da ita a Chana, domin nuna wa ‘yan Najeriya cewa Chana fa ba Najeriya ba ce.

Da aka tambaye shi yadda ake samun takun-saka da kuma difilomasiyyar rainin-wayo da wasu kasashe ke wa Najeriya, Wali wanda ya shafe shekaru biyar ya na Jakadancin a Chana tsakanin 2009 zuwa 2014, ya ce a baya Najeriya na da kwarjini sosai a idon duniya, musamman ma Afrika.

“Domin a da ko wata matsaya kasashen Afrika za su dauka, to sai sun jira su ji ta bakin Najeriya tukunna.”

An tambaye shi yadda ake yawan samun rahotannin kuntata wa ‘yan Najeriya a wasu kasashe. Wali ya nuna cewa lokacin da ya na Chana ya sha warware irie-iren wadannan matsaloli da dama.

“Yawancin ‘yan Najeriya masu shiga matsala a Chana, Afrika ta Kudu, Indonesia, Thailand da Malaysia da sauran sassan kasashe, su ke janyo wa kan su.

“Mun sha faman nuna musu yadda abubuwa su ke. To kuma abin da na kara fahimta shi ne, wadannan kasashe su ka yi wa ‘yan Najeriya irin abin da ake wa ‘yan kasar su ne a nan Najeriya.

“Kusan kashi 90% na matsalolin da ƴan Najeriya ke shiga a ƙasashen nan, duk laifuka ne da suka danganci safarar ƙwayoyi.

Yanzu haka akwai dandazon ƴan Najeriya na tsare a kurkukun wadannan kasashe da dama.

Makonni biyu da su ka gabata ma PREMIUM TIMES HAUSA ta buga hira da Aminu Wali, inda ya yi bayani kan dalilin da ya sa Najeriya ba ta samun dauki daga kasashen Turai.

Tsohon Ministan Harkokin Waje, Aminu Wali, ya bayyana dalilin da ya sa manyan kasashen duniya ba su kawo wa Najeriya dauki wajen yaki da Boko Haram.

Wali ya taba zama Wakilin Dindindin na Majalisar Dinkin Duniya, kuma shi ne Ministan Harkokin Waje tsakanin 2014 zuwa 2015, lokacin rubdugun hare-haren Boko Haram.

Da ya ke amsa tambaya daga PREMIUM TIMES, Wali ya ce gwamnati kan yi asarar rashin samun dauki daga manyan kasashen duniya, sau da yawa saboda yanayin irin adawar da ‘yan adawa ke wa gwamnati a cikin gida.

Ya ce kasashen duniya sun fi gaskata kalaman masu adawa da gwamnati, wadanda kan haddasa toshe wa kasa wasu damammaki, hana ta wasu dauni da kuma kakaba mata takunkumi zuwa maida ta ware-ga-dangi.

Ya ce irin wannan misalin ya faru a lokacin da ya ke Ministan Harkokin Waje.

“Idan ana maganar tsaro, to su jam’iyyun adawa sun fi bada karfi wajen caccakar gwamnati, ba ta hanyar bada shawara da goyon baya ba.”

Ya ce to kasashen Turai sun sha rungumar soke-soken da masu adawa ke yi na farfaganda a lokacin mu, har mu ka shiga matsala da su.

Share.

game da Author