Ƙungiyoyin Afenifere da Ohanaeze Ndi-Igbo sun shiga faɗan Obasanjo da Fadar Shugaban Ƙasa

0

Ƙungiyar Kare Muradin Ƙabilar Yarabawa Zalla (Afenifere) da ta Ohanaeze Ndi-Igbo, Kungiyar Kare Muradin Gurguzun Kabilar Igbo, sun ragargaji Fadar Shugaban Ƙasa, bayan da fadar ta yi magana kan taron da ƙungiyoyin su ka yi da Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Ƙungiyoyin da suka hada har da Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta Niger Delta Forum da Middle Belt Forum, sun ce Fadar Buhari ta nuna rashin dattako da har ta maida wa Obasanjo raddi.

Cikin sanarwar da suka fitar a ranar Litinin, sun ce kamata ya yi a dauki kakkausan bayanan da Obasanjo ya yi a matsayin wani jan hankali da hannun-ka-mai-sanda ga gwamnati, maimakon fadar ta kidime wajen maida wa Obasanjo raddi.

Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Obasanjo ya ce Najeriya ta lalace kuma rabuwar kawunan al’ummar kasar nan ya kara zurfi sosai a karkashin mulkin Buhari.

Sai dai kuma a martanin da Fadar Shugaban Kasa ta maida wa Obasanjo ta hannun Kakakin Buhari, Garba Shehu, ta ce “Obasanjo ne Babban-Kwamandan-Raba-Kawunan ‘Yan Najeriya.”

Sannan kuma fadar ta fatattaki kungiyoyin biyar da suka gana da Obasanjo.

Sai dai kuma a ranar Litinin, kungiyoyin sun fitar da sanarwa cewa sun ji dadin yadda suka taru, inda su ka tattauna mafita daga mawuyacin halin da kasar nan ke ciki.

“Shugabannin Yanzu Sun Yi Nisa Ba Su Jin Kira”- Inji Kungiyoyi

Cikin sanarwar da su ka fitar ranar Litinin, sun ce, “Lallai shugabannin yanzu sun yi nisa, ba su jin kira, kuma ba su yarda sun yi kuskure. Sun dibge har ma ba su san cewa murdadden halin da kasar nan ke ciki, wani babban hatsari ne ba.”

Sun ce su na mamakin yadda Fadar Shugaban Kasa ke barin jaki ta na dukan taiki dangane da matsalolin da aka nuna mata masu yi wa kasar nan da tattalin arzikin ta barazana.

“To mu dai ba za mu fasa fitowa mu na haduwa mu na tattauna don tattauna matsalolin da suka dabaibaye kasar nan. Tare kuma nusasshe da ‘yan baya matasa, manyan gobe halin da kasar nan ke ciki ba.”

Sun ce idan Fadar Shugaban Kasa ba za ta saurari koke-koken jama’a ba, to hakkin su jama’a din ne su ci gaba da tambayar shin me ita gwamnati ke yi wajen kokarin warware wadannan matsalolin?

“Ya kamata Fadar Shugaban Kasa ta sani cewa kungiyoyin mu ba ‘yan amshin-Shatan Obasanjo ba ne. Kuma ba Fadar Buhari ce za ta fada mana irin yadda za mu yi korafin kuncin da mu ke ciki a fadin kasar nan ga Shugaba Muhammadu Buhari ba.”

Share.

game da Author