Ƙungiyar ActionAid ta roki jihohi su kafa Hukumar Inganta Rayuwar Naƙasassu

0

Biyo bayan naɗa wa sabuwar Hukumar Inganta Rayuwar Naƙasassu Shugabannin Gudanarwa da Babban Sakatare da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, Ƙungiyar ActionAid ta nemi kowace jiha ta kafa irin wannan hukumar.

Cikin sanarwar da kakakin yaɗa labarai ta ƙungiyar, Nihilola Ayanda ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta ce ya zama wajibi jihohi su bi sawun gwamnatin tarayya wajen ganin an haka guiwa, an kyautata rayuwar naƙasassu a ƙasar nan.

ActionAid ta ce gwamnatin tarayya ta yi ƙoƙari, ganin yadda aka kafa dokar da ta tabbatar da hukumar ta naƙasassu. Ta ce yanzu abin da ya rage shi ne a rika bijiro da ayyuka da tsare-tsaren cikin ƙasa waɗanda za su riƙa inganta naƙasassu.

Sannan kuma ta ce gwamnati ta riƙa tunawa da naƙasassu a dukkan shirye-shiryen samar ka kayan more rayuwa da ayyuka, tsara birane, tsarin sufurin motocin haya da sauran su.

Ministar Agaji, Jinƙai da inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Farouq ce ta yi rawar ganin cewa kafa hukumar ya tabbata.

Sannan kuma hukumar yanzu haka a karkashin ma’aikatar ta ta ke.

Hukumar Naƙasassu: Na cika alƙawari, inji Minista Sadiya

Ministar Harkokin Agaji Da Jinƙai, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa a yanzu sabuwar Hukumar Naƙasassu ta ƙasa, wato ‘National Disability Commission’, ta riga ta kafu bayan amincewa da naɗa shugabannin ta da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2020.

A cikin wata sanarwa da hadimar ta a ɓangaren aikin jarida, Halima Oyelade, ta bayar a ranar Alhamis, ministar ta ce tun daga naɗin ta a bara ta sha alwashin tabbatar da ganin an kafa wannan Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa kuma ta fara aiki.

Ta ce, ‘’Wannan ranar farin ciki ce a gare ni wadda buri na ya cika, ganin cewa wani sashe na mutane masu matuƙar buƙatar tallafi wadanda na ke jin tausayin su, a ƙarshe sun samu hukuma tasu ta kan su, har an naɗa mata shugabanni waɗanda za su tafiyar da al’amurran ta, kuma ta kare hakƙoƙin su, sannan ta sama masu kyakkyawan yanayi da za su inganta rayuwar su har su bada tasu gudunmawar ga cigaban al’umma baki ɗaya.”

Ministar ta mika godiyar ta ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari saboda rattaba hannu da ya yi kan Dokar Hana Nuna Wariya Ga Naƙasassu ta Shekarar 2019 a bara, wadda ta bada damar a kafa hukumar.

Sadiya Farouq ta ce: ‘’Ta hanyar amincewa da nadin shugaba da Babban Sakatare da sauran membobin cibiyar gudanarwar hukumar, Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara nuna sadaukarwar sa ga batun inganta rayuwar mutane marasa galihu a Nijeriya, kuma ya ba su damar su ma su ci moriyar dukkan hakkokin su a matsayin su na ‘yan Nijeriya.”

Ta taya murna ga nakasassun da ke Najeriya wadanda ta ce yawan su ya kai mutum miliyan 30 saboda wannan babbar nasara da aka samu, kuma ta yi kira a gare su da su yi amfani da wannan dama da aka sama masu.

Sadiya ta ce: “Ina taya murna ga ‘yan’uwa na maza da mata wadanda ke rayuwa da wata nakasa a Najeriya saboda wannan cikar buri, kuma ina kira a gare ku da ku yi amfani da damar samun wannan hukuma wajen haɗa kan ku don gina rayuwa mai albarka.”

Har ila yau, ministar ta taya murna ga shugabannin hukumar da aka naɗa tare da yin kira a gare su da su yi aiki tuƙuru.

Ta ce, “Ina taya ku murna sosai, kuma ina kira a gare ku da ku dauki wannan wannan nadi naku a matsayin wata dama da ku ka samu ta zama shugabanni na farko na hukumar, don haka ku shimfida fandeshi mai ƙarko na hukumar, tare da tunanin cewa samun ingancin rayuwar mutum sama da miliyan 30 da ke fama da nakasa a Nijeriya yanzu ya danganta kan yadda ku ka aiwatar da aikin ku.”

Da zaran Majalisar Dattawa ta amince da nadin, hukumar za ta shiga aiki gadan-gadan, inji ta.

Minista Sadiya ta ce, “Ayyukan hukumar sun hada da fito da tsare-tsare da manufofin da su ka dace tare da aiwatar da su don ilmantar da nakasassu da kyautata rayuwar su; tsara hanyoyin inganta rayuwar naƙasassu, da kuma kyautata rayuwar su ta hanyar sauya tunanin mutane su daina yi wa nakasassu kallon banza.”

Share.

game da Author