Bayan shiri tsaf da ƙungiyar Ƙwadago da wasu kungiyoyin kula da kare hakkokin ma’aikata da suka yi na fara yajin aiki a yau Litinin 28 ga Satumba, an samu daidaituwa a tsakanin su da gwamnati.
Idan ba a manta ba a kokarin da Gwamnati Tarayya ke yi domin ganin Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC ba su barke zanga-zanga yau Litinin da kuma zarcewa yajin aiki ba, an yi wani taron gaggauwa tsakanin kungiyoyin da kuma Gwamnatin Tarayya.
Taron wanda aka yi ranar Lahadi daga karfe 7 na yamma, an shafe tsawon dare ana yamutsa gashin baki tsakanin bangarorin biyu.
Ƙungiyar Ƙwadago dai ta yanke shawarar tafiya yajin aiki da zanga-zanga ne bayan gwamnatin Buhari ta kara kudin fetur da kudi wutar lantarki.
Takura biyu da aka yi cikin makon da ya gabata domin ganin an shawo kan ‘yan kwadago bai yi nasara ba. Saboda sun ce sai gwamnati ta janye karin da ta yi sannan za ta janye yajin aiki.
Ministan ƙwadago ya shaida cewa gwamnati da ƙungiyoyin sun amince da wasu matakai da za dauka domin warware matsalolin.
Chris Ngige ya ce, gwamnati za ta cigaba da zama da ƙungiyoyin ƙwadago domin a cimma matsaya guda a tsakanin su.
Kwamitin sun hada da ministoci da manyan jami’an hukumomin gwamnati da abin ya shafa.