ƘAƘUDUBA: Kotu ta hana Shoprite kwashe kadarori daga Najeriya, saboda bashin dala milyan 10

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ta ƙi sauraren uzirin neman janye dabaibayin da ta yi wa katafaren kantin zamani, Shoprite, wanda ta hana ya kwashe kadarorin sa daga Najeriya, saboda ana bin sa bashin dala milyan 10.

Shoprite ya garzaya kotu inda ya nemi Mai shari’a ya janye ɗaurin-talalar da ya yi wa kantin na hana shi wasu mu’amaloli da Kadarorin na sa.

Mai Shari’a Nicholas Oweibo, ya ce tunda yanzu kotuna duk hutu su ke yi, ba zai iya sauraren bukatar Shoprite ba, sai dai ya bari a dawo hutu tukunna.

Ya ce Cif Jojin Kotun Ɗaukaka Ƙara, John Tsoho ya fitar da sanarwa ga alƙalai cewa kada a yi zaman wata shari’a a cikin hutu, sai dai ts musamman da ta hada da batun shari’ar jirgin ruwa da sauran wata wadda batun Shoprite ba ya ciki.

Ranar 4 Ga Yuli ne Mai Shari’a Mohammed Liman na Babbar Kotun Tarayya a Lagos ya yanke hukunci a kan karar da wani kamfani mai suna A.I.C Limited ya kai Shoprite a gaban sa.

Hukuncin ya nuna cewa, kotu ba ta yarda Shoprite ya kwashi dukka ko wani bangare na kadarorin sa ko karkatar da wasu kudin sa da ke nan zuwa wani wurin da Kotun Najeriya ba ta da hurumi ba.

Ba a kuma yarda a sayar ko a bayar da aro, jingina ko kyautar da wata kadara ta Shoprite ba.

Kuma ba a yarda a yi canjin suna ko sauyin hakkin mallakar wata ko wasu kadarorin Shoprite ba, har sai an ji hukumcin da kotu ta yanke tukunna.

Sannan kuma an umarci Shoprite su bai wa kotu jadawalin kididdigar Harkokin cinikin su kakaf na shekarun 2018 da na 2019.

Cikin shekarar 2018 ne kamfanin A.I.C ya maka Shoprite kara kotu, ya nemi a biya shi dala milyan 10 wadda kantin ya karya ka’idar yarjejeniya.

Cikin watan Yuli PREMIUM TIMES ta buga labarin aniyar Shoprite na kwashe kadarorin sa daga Najeriya ya daina kasuwanci a kasan nan.

Katafaren kantin zamani mallakar ƴan Afrika ta Kudu da ke da reshe a Najeriya, Shoprite, ya bayyana sanarwar shirye-shiryen ficewa daga Najeriya ba da dadewa ba.

Haɗaɗɗen Rukunin Kantunan Shoprite, Shoprite Holding Limited ne ya yi wannan sanarwa a safiyar Litinin, inda ya ce sun ɗauki wannan mataki ne tun bayan nazarin da suka yi na jimillar cinikin karshen shekara a ranar 28 Ga Yuni, 2020.

Shoprite, wanda katafaren kantin zamani ne da ke da rassa a kasashen duniya, ya ce duk da killace jama’a da aka yi a Najeriya saboda Coronavirus, cinikin su ya karu da kashi 6.4% a wannan shekara, wato kudin Afrika ta Kudu R156.9.

Sai dai sun ce lura da masu bukatar da ke son sayen kadarorin su ne ya sa za su janye daga Najeriya, kamar yadda za su tashi daga wasu kasashe na Afrika.

Sai dai kuma sun ce duk da cewa cinikin da ake yi a Najeriya bai ragu ba, kamar yadda ake yi kafin cutar Coronavirus, to shi kan sa cinikin ba wani abin a zo a gani ba ne.

“Za mu sayar da komai mu tarkata na mu mu bar Najeriya. Saboda a Najeriya mu na da kantama-kantaman kantina 26 a jihohi 8 har da Abuja. Sannan mu na da wasu kantinan a wasu kasashen Afrika ta Kudu. Amma gaba dayan cinikin da aka yi a Najeriya da sauran kasashen Afrika, bai fi kashi 11.6 na gaba ɗayan cinikin da Shoprite ya yi a Afrika ta Kudu kaɗai ba.”

Sun bayyana sakwarkwacewar cinikin su a kantinan su da ke kasashen Afrika da sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus, wadda ta haddasa: “killace jama’a cikin gida, rufe kantuna a duniya, nesantar juna yayin mu’amaloli, takaita zirga-zirgar jirage da motoci, takaita zirga-zirgar jama’a, takaita lokutan bude kantina, takaita ma’aikata da sauran su.”

Shoprite sun bude kantin farko a Najeriya cikin Disamba, 2005. Amma yanzu su na da kantina 26 a cikin jihohi 8 har da Abuja.

Cikin sanarwar su na fara shirin barin Najeriya, Shoprite ya ce ya dauki ƴan Najeriya har sama da 2,000. Kuma ya gina kyakkyawar mu’amalar kasuwanci da dillalan kayan masarufi, manya da kananan masu hada-hada da kuma manoma sama da 300.

Share.

game da Author