Zan rungumi mai Korona, in yi masa tofi ya warke garau, ni ma garau – Fasto Oyedepo

0

Fitaccen mai wa’azi kuma Shugaban Cocin Living Faith, David Oyedopo, ya bugi kirjin cewa zai iya rungumar mai cutar Korona da hannuwan sa, har ma ya yi masa numfashi, idan aka kawo majiyyacin don ya yi masa addu’a

Oyedepo ya bayyana haka a lokacin da ya ke wa’azin bushara a cocin sa karshen makon nan.

“Shin ku na tsammanin idan aka kawo min mai dauke da cutar Korona, ba zan iya kama shi da hannu na har na yi masa addu’a ba. Ku na tsammanin har sai na tsaya sanya safa a hannaye na kafin na kama mai cutar Korona na yi masa addu’a?

“Zan rungume shi da hannnaye na na yi masa numfashi, sannan na yi masa addu’a.”

Kamar yadda aka yi tsammani, wannan ikirari na sa ya tayar da kura, har aka rika ce-ce-ku-ce a tsakanin mambobin cocin sa da kuma sauran jama’a.

Ba wannan ne karon farko da fasto Oyedepo ya fara jangwalo wa kan sa surutai a kan cutar Korona ba.

Ranar 28 Ga Yuni, faston ya rika yin fankamar cewa cocin sa ya warkar da masu cutar Korona har mutum 114.

Sannan ya kara cewa mutanen Lagos da Ogun sun kamu da cutar kin zuwa coci ce ba cutar Korona ba.

Oyedepo ya kuma tsine wa kulle coci-coci da aka yi da sauran wuraren ibadu da gwanonin Lagos da Oyo su ka yi.

Tir Da Masu Rufe Baki Da Hanci Saboda Korona – Oyedepo

Oyedepo ya ragargaji masu daura kyallen rufe baki da hanci, saboda tsoron kamuwa da cutar Korona. Haka ya rika yi musu fata-fata a cikin wani sabon bidiyo da ya fitar.

“Za ka daura komai tamkar wani likita. Ka na tafiya kamar wadda ke cikin fargabar kai masa farmaki. Wata rana za su gane cewa abin duk yaudara ce aka rika yi musu.

“Ahaf! Nan gaba za su gane ashe abin duk yaudara ce kawai aka rika yi musu.” Haka Oyedepo ya fada, tare da shakku kan matakan da aka ce su ne ke hana kamuwa daga daukar cutar Korona.

“Ka wani rufe bakin ka. Shin da ka ke cin abinci ka rufe bakin ka? Ko kuwa babu Korona a lokacin da ka ke cin abinci ne? Ni dai sai na kalli abin, na ce shin wannan wace irin shegantaka ce?”

Ya ce matakan hana kamuwa da cutar Korona ba na Allah ba ne, duk Shaidan ne ya kawo su domin ya nukurkusar da zukatan dan Adam.

“An ce kada ka kusanci tsofaffi, amma kuma ka na sayen abincin da su ke sayarwa.

“Shin idan za ka sayi daga hannun wata gyatuma, ka na tambayar ta yawan shekarun ta ne? Ka yi min wannan tambayar ai na yi maganin ka.

“Cutar Korona ba za ta taba zama dalilin hana ka gudanar da ibada ko nesanta ka daga kusantuwa da Ubangiji ba.”

Shi ma Shugaban Cocin Christ Embassy, Chris Oyakhilome, ya ragargaji yadda Gwamnatin Tarayya ta kirkiro hana jama’a zirga-zirga, ta yadda masu halartar coci-coci suka yi karanci sosai.

Share.

game da Author