Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tabbatar wa shugabannin kungiyoyin addinin musulunci da suka ziyarce shi cewa a shirye yake ya sa hannu a hukuncin da kotu ta yanke na kisan mawakin da ya yi wa annabi SAW izgilanci.
Idan ba manta ba mawaki Yahaya Shariff Aminu ya yi wani waka da ya aibata manzon tsira SAW. Hakan yasa matasa sun yi kokarin banka wa gidan mahaifin sa wuta.
Daga baya mahaifin Shariff ya ce bashi ba shariff duk abinda kotu ta ga dama ta yi masa.
Ganduje ya ce wannan hukunci yayi daidai domin babu wanda zai wayi gari kawai dan ya isa ya rika yin izgilanci ga manzon tsira kuma a zuba masa ido. Sannan kuma ya ce wannan hukunci zai zama darasi ga wasu.
” Idan ya daukaka kara, za mu jira koda ko kotun koli ya tafi, za mu jira shi. Zan kuma saka hannu a zartar masa da hukuncin kisa kamar yadda kotun shari’ar musulunci ta yanke.
Malaman addini da suka ziyarci gwamnan sun yaba wa kotun musuluncin da ta yanke wannan hukunci sannan sun bayyana cewa suna tare da gwamna Ganduje 100 bisa 100 kan wanna hukunci da aka yanke wa Sharrif.
” Tabbatar da wannan hukunci zai jaddada inganci da karfin kotun shari’ar musulunci a jihar da kasa baki daya.
Discussion about this post