ZAMFARA: An samu rahotanni 160 kan lalata kananan yara maza da mata da kuma fyade

0

Cibiyar Tuntubar Rahotannin Lalata Kananan Yara Da Fyade ta Jihar Zamfara (SARC), ta bayyana cewa a cikin shekara daya ta samu rahotonni har guda 160 na lalata yara maza da yara mata da kuma fyade cikin shekara daya a Jihar.

Shugaban cibiyar Ahmed Shehu, shi ne ya yi wannan bayani a lokacin da ya karbi mambobin Majalisar Kananan Yaran Jihar Zamfara, wadanda suka kai masa ziyara.

Wata kungiya mai zaman kan ta ce mai suna ‘Save the Children International’, ta dauki nauyin rangadin ziyarar da majalisar yaran ta yi zuwa wannan cibiya da kuma Gudan Tsare Kangararrun Yara.

Shehu ya ce rahotannin da suka samu na yawan lalata kananan yara da fyade, akasari duk kananan yara ne ake afkawa da kuma yaran da suka dan tasa, amma ba su kai shekaru 20 ba.

Ya bayyana yawan lalata yara maza da yara mata da kuma fyade a Zamfara cewa abin tayar da hankali ne matukar gaske.

“Mun samu rahoton wani uba wanda ya yi lalata da ‘yar cikin sa, ‘yar shekara hudu.” Inji Shehu.

“Mu na matukar bukatar hadin kan gwamnati da sauran jama’a, musamman a cikin unguwanni.”

Shehu ya kara da cewa cibiyar sa na fuskantar babban kalubale na karancin kudade, inda ya kara yin nuni da cewa matsalar kudade na kawo wa cibiyar barazanar kasa gudanar da ayyukan ta da suka rataya a kan ta.

“Maganar gaskiya mu na matukar fuskantar karancin kudade da kuma karancin wuraren kwanciya.

“Mu na bukatar gwamnati ta kara inganta wannan cibiya, musamman a kara fadada ta, yadda za a kara yawan yaran da ake kaiwa a cibiyar, wadanda karti maza ke lalatawa.

Ya gode wa Ma’aikatar Harkokin Shari’a, Lafiya da ta Harkokin Mata da Kananan Yara na Jihar Zamfara, dangane da kokari da gudummawa da goyon bayan da suke bai wa cibiyar.

Shehu ya gargadi iyayen yara su kara kula da sa-ido sosai a kan yaran su kanana.

Ya kuma yi kira ga iyayen da aka yi wa yaran su fyade su daina boyewa, su rika kai rahoto, domin daukar mataki.

Kakakin Majalisar Kananan Yara, Sumayya Aninu-Aliyu, ta ce sun kai ziyarar ce domin sani da kuma ganin irin halin da yaran ke ciki.

Share.

game da Author