Zaman barzahu (kabari) babu makawa, amma wace irin zama mu ke yi ma kanmu tanadi? Daga Mukhtar Umar Lere

0

Gama garin mutum shine wanda tunaninsa kashi 90 cikin 100 shine ya ya zai samu ko tara abin duniya. Ya tallaƙa tunani, nema da tarawa kawai akan abin duniya kamar za’a rayu a duniya har abada.

Da yawa cikin masu haɗaman tarawa da taskace arzikin duniya sukan manta da inda wasu dukiyoyin su ke saboda yawansu, musamman waɗanda suka daɗe muna kwasa daga Baitul Mali, duk Gwamnati sai ta yi da su. Suna da danƙararrun gidaje a Dubai, Amerika, Ingila, a manyan biranen ƙasan nan basu da adadi, ga hanyoyin shigan kudi kala-kala, amma kabarinsu ba su damu da gina shi ba sam.

Mafi abin tausayi a duniya shine talaka mara himman Addini, yana fama da talaucin duniya kuma yana neman ya yi na Lahira. Yana da faraga na isashshen lokaci, amma yaƙi tsayawa ya koyi Addini ya yi aiki tuƙuru wajen neman arzikin Lahira tunda yana cin jarabawan talaucin duniya. Subhan-Allah!

Zaman duniyar nan ɗan taki ne kawai. Saboda haka, kada ƙyalƙyalin duniya ya tsole maka ido sai ka tara da yawa ko ta hanyar ha’inci da cuta domin ka ji daɗin zaman duniya. Ɗan kaɗan na halal mai albarka zai kawo kwanciyar hankali da wadatan zuci saɓanin mai yawa na algus mai dauwamad da tashin hankali a duniya da Lahira.

Zaman da mutum zai yi a labari ya ninka na duniya ninki da yawa. Mutum bai yi shekara 100 a duniya ba, amma sai ya yi ɗaruruwa ko dubbai a kabari, kamar yadda waɗanda suka yi zamani da Annabi Adam (AS) suka yi shekaru dubbai suna jiran Qiyamah ta tsaya a cikin kaburburansu.

Saboda haka kada mutum ya ɓata lokacinsa a banza a duniya, wacce zaman kabari kawai kafin a tafi Lahira zai manta ya yi rayuwar duniya.

Duk Musulmi ya san mun zo duniya ne domin bautawa Allah Shi kaɗai, kuma bautar nan ba za ta yiwu ba sai an yi karatun fahimtar Addinin bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW), sannan a yi aikin Ibadu da ikhilasi. Bautar Allah da jahilci aikin banza ne, kamar mai gona ne da ya shuka dusa yana jiran tsiranta. Idan mutum bai san Allah ba sai ya yi ta yin wargi da al’amuran Allah da Addini, shi ya sa Allah Ya hukumta lallai sai an san Shi kafin a bauta maSa.

Allah Ya ƙara mana karsashin dagewa wajen gina kabarinmu da Lahiranmu, domin nan ne matabbata, Ameen.

Share.

game da Author