A shirye shiryen bude makarantu da gwamnatin jihar Kano ke yi don daliban ajin Karshe su rubuta jarabawa, Gwamnatin jihar za ta yiwa makarantun sakandare 528 na gwamnati da masu zaman kansu feshin maganin kashe kwayoyin cuta a jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sa’id ya sanar da haka a taron manema labarai ranar Litini a garin Kano.
Sa’id ya ce gwamnati ta tsayar da ranar 10 ga watan Agusta ranar da daliban dake ajin karshe wato SS3 za so koma makaranta domin shirin fara rubuta jarabawa WAEC da za a fara ranar 17 ga Agusta.
Ya Kuma ce gwamnati ta bai wa shugabanin makarantu da masu makarantu masu zaman kansu kwanaki 7 domin saka matakan guje wa kamuwa da Korona a makarantun kafin dalibai zu fara dawowa.
Bayan haka ma’aikatar kiwon lafiya za ta raba wa dalibai takunkumin fuska, man tsaftace hannu da kayan Kare ma’aikacin lafiya daga kamuwa da cutar a wadannan makarantu.
Sannan kuma gwamnati zata yi wa dukka daliban da zasu rubuta jarabawar a jihar gwajin cutar Korona kafin su shiga aji.
Gwamnati ta kuma tsara dokoki kamar haka:
1. Makarantun ba za su fara aiki ba sai ranar 10 ga watan Agusta amma daliban dake makarantun kwana za su iya komawa makaranta ranar 9 ga wata.
2. Za a rage yawan awowin da ake koyar da dalibai darussa zuwa awa hudu.
3. Makarantu za su tanadi na’urar gwajin yanayin jiki, wuraren wanke hannaye da ruwa da sabulu a ko ina a makarantun da hana dalibai taruwa wuri daya a makaranta.
4. Makarantun dake zaman kansu za su karbo takardan dokoki da sharaddun guje wa kamuwa da cutar da gwamnati ta bada a hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano.
5. Makarantun gwamnati za su karbo takardan izinin bude makaranta a hukumar kula da makarantun sakandare na jihar Kano.
Dalibai 11, 046 ne za su rubuta jarabawar kammala sakandare a makarantu 528 a jihar
Gwamnati za ta sanar da ranar da sauran dalibai za su dawo makaranta a jihar, amma kafin haka dalibai za su ci gaba daukar darasi ta yanar gizo.