Rundunar ‘Yan sandan jihar Adamawa, ta damke wasu matasa biyu da ake zargin su da laifin yi wa wasu mata biyu fyade.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Sulaiman Nguroje, ya shaida cewa ya damke wadannan matasa ne a unguwar Jambutu dake karamar hukumar Yola Ta Arewa.
” Wadanda aka kama sun hada da wani matashi dan shekara 19 mai suna Aminu Abdullahi da wani Abubakar Haruna, 32. Aminu yayi wa wata ‘ya shekara 9 fyane, shi kuma Abubakar yayi wa ‘ya shekara 15.
Shi Aminu ya yi lalata da wannan yarinya ce a wani kangon gine dake kusa da filin kwallon Jambutu, shi kuma Abubakar ya yi lalata da ‘yan makwabcin sa ne.
A karshe Nguroje, ya ce tuni am mika su ga hukumar ladabtar da masu aikata irin wannan laifi, sannan kuma ‘yan sanda na ci gaba da bincike.
Discussion about this post