‘Yan sanda sun damke Faston da ya yi wa Ya da Kanwa ciki

0

‘Yan sandan jihar Ogun sun damke wani Fasto mai suna Ebenezer Ajigbotoluwa da ake zargin yi wa Ya da Kanwa ciki sannan da damfarar uwar su naira miliyan 2.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya shaida cewa mahaifiyar wadannan ‘yan mata biyu ne ta kawo kara caji ofis.

” Shi dai wannan fasto ya yi alkawarin warkar da wadannan yan mata ne daga shaidanun aljanu da suka shafe su. Daga nan sai ya umarci mahaifiyar su ta dawo da iyalanta kaf harabar cocin domin aiki yayi kyau sannan ya ce ta bashi naira miliyan 2 domin aiki za a yi sosai.

” Mahaifiyar wadannan ‘yan mata kuwa sai ta bashi wannan kudi da ya nema. Daga nan sai Fasto ya rika yin lalata da ‘yan matan duka su biyu. Ana haka ne ne fa ciki ya shiga.

Daga nan sai fasto ya nemi a zubar da cikin. Da ya ga asirin shi ya tonu sai ya gudu ya bar wannan coci da gari.

Aka yi ta neman sa har Allah yasa ‘yan sanda suka cafke shi.

Rundunar ‘yan sandan ta shaida cewa lallai ta an sami kayan tsafe-tsafe a dakunan wannan fasto kuma ya amsa kusan duk abin da ake zargin ya aikata.

Share.

game da Author