Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke mahara 27 da suka buwayi mutane da sace-sace da garkuwa da mutane a jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda Bola Longe wa manema labarai haka a garin Lafiya ranar Litini.
Longe ya ce jami’an tsaro sun kama wadannan mahara makonni biyu da suka gabata a wurare dabam-dabam a jihar.
Ya ce a cikin maharan da aka Kama akwai maharan da suka kashe dagacen kauyen Odu Amos Obere .
” An cafke wadannan mahara a mashaya suna duldular barasa suna shan farfesu a wani dandali holewa daka Nasarawa.
Longe ya ce maharan sun tabbatar wa jami’an tsaro cewa sune suke yi garkuwa da matafiya a Otukpo zuwa Abuja sannan sun kashe ma’aikacin hukumar NIS Salisu Usman-Maku da ‘yar uwar sa Sa’adatu Usman-Maku a Gidi dake karamar hukumar Akwanga.
Longe ya ce rundunar ta Kama maharan da suka yi garkuwa da shugaban kungiyar CAN na jihar Nasarawa Joseph Masin.
Ya ce an same su da bindigogi, harsasai da dama da mota guda daya.
Idan ba a manta ba a ranar 3 ga watan Agusta ne jami’an tsaron jihar ta lashi takobin kamo maharan da suka kashe dagace kauyen Odu Amos Obere.
Maharan sun kashe basaraken ne a wani harin bazata da suka kai masa har fadar da misalin karfe 10 na daren ranar 31 ga watan Yuli.
Basarake Obere ya rasu a asibiti duk da kokarin da likitoci suka yi na ceto ran sa.