Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa farashin kayan abinci da suka hada da doya, shinkafa, tumatir da kwan kaji sun tsula tsada a cikin watan Yuni.
Cikin wani rahoton da NBS ta buga a shafin ta na yanar gizo, ta bayyana tsadar a cikin rahoto mai suna “Rahoton Farashin Wasu Kayan Abinci na Yuni 2020.
An tababtar da tashin farashin kilogiram din tumamir da kashi 30.25 bisa 100 na farashin sa da aka sani ba baya.
Tun a cikin watan Mayu farashin tumatir ya tashi daga kilo daya a kan naira 278.23 zuwa 294.46 cikin Yuni, wsto karin kashi 5.84 kenan.
NBS ta ce an samu karin kashi 35.97 ga farashin shinkafar da ake shigowa da ita daga waje.
Kilo daya na shinkafa ya tashi daga naira 463.21 cikin Mayu zuwa naira 479.74 a cikin Yuni. Wato karin kashi 3.57 kenan.
Shinkafa kusan it’s ce abincin da aka fi raja’a da shi a Najeriya. Sai dai kuma duk da haramta shigowa da ita daga kan iyakokin kasar nan, akwai ta ana sayarwa ko’ina a kasar nan.
Shi ma farashin kilo din doya ya karu a cikin watan Yuni, zuwa kashi 37.63 cikin Yuni.
Doya guda daya karama ya tashi daga naira 236.90 zuwa 250.70 a cikin Yuni.
Ba kamar sauran kayan abinci ba, farashin kwan kaji kwaya raguwa ya yi. NBS ta ce idan aka kwatanta farashin kwan kaji da watan Yuni, za a ga cewa farashin sa raguwa a lissafin dozin idan aka kwatanta da Yuni 2019.
Cikin Yuni ya tashi daga naira 426.46 zuwa naira 479.74. Wato karin kashi 2.24 kenan.
NBS ta ce ta watsa ma’aikatan ta 700 a fadin jihohin kasar nan su ka gudanar da wannan binciken tare da masu yi musu duba-gari da masu sa-ido daga ciki da wajen NBS.
Ta ce an tattara farashin daga kananan hukumomi 774 na kasar nan, inda aka yi wa sama mutum 10,000 tambayoyi.