Yadda sojoji suka darkake ‘yan ta’adda a dazukan jihar Neja

0

Kodinatan yada labarai na Ma’aikatar Tsaron Najeriya, John Enenche ya ce dakarun sojoji dake karkashin ‘Operation Lafiya Dole’ sun kashe ‘yan ta’adda da dama a kauyen Tashan Kare dake jihar.

Enenche ya bayyana cewa dakarun sun yi amfani da bayanan sirri game da ayyukan wadannan mahara.

” Daga nan ne fa aka gaggauta tura sojoji inda suka yi arangama da wadannan ‘yan ta’adda suka kashe na kashewa wasu kuma suka arce.

Sai dai Kuma sojoji biyar sun ji rauni a wannan bata kashi.

Enenche ya ce hakan da dakarun suka yi na daga cikin gagarimin shirin kakkabe ta’addanci baki daya da ake yi a yankin Arewa ta Tsakiya.

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da mutuwar wani bature da mahara suka yi garkuwa da shi da wani dan Najeriya tsakanin kauyukan Yankila da Regina a karamar hukumar Rafi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Usman ya bayyana cewa jami’an tsaro sun tsinci gawar baturen a dajin Pangu Gari dake karamar hukumar Rafi.

Ya ce an Kai gawar babban asibitin Minna domin gudanar da bincike a kai.

Usman ya ce yanzu dai jami’an tsaro na gudanar da bincike domin ceto dan Najeriyan dake hannun masu garkuwa da mutane.

Ya yi kira ga mutane musamman wadanda ke da bayanan da za su taimaka wajen kamo masu wadanda suka yi garkuwa da su.

Idan ba a manta ba rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana garkuwa da akyi da wadannan mutane.

Kwamishinan ‘yan sanda Adamu Usman ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Minna ranar Talata.

Adamu ya ce dan kasar wajen da dan Najeriyan na aiki da Kamfanin ‘Transparent construction’ dake gyaran babban titi a yankin.

An yi garkuwa da wadannan mutane ranar 17 ga watan Agusta da karfe 11:05 na dare.

Ya ce rundunar bata da masaniyar aiyukkan da Kamfanin ke yi a yanki amma an aika da jami’an ta domin ceto da kamo wadanda suka yi garkuwa da mutanen.

An tabbatar cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da su a wurin aikin wata rijiyar danyen man fetur a Abua, dake jihar.

Gamayyar jami’an tsaro na JTF da aka tura yankin Neja-Delta domin kula da tsaron rijiyoyin mai sun tabbatar da sace Turawan su biyu.

Share.

game da Author