Yadda safarar mutane ke cigaba da yada cututtukan sanyi da Kanjamau a duniya – UNFPA

0

Hukumar UNFPA ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa daya daga cikin hanyoyin da cututtuka ke yaduwa a duniya musamman cututtukan sanyi da kanjamau a duniya itace ta hanyar safarar mutane da ake yi zuwa kasa-kasa.

Shugaban hukumar Natalia Kanem ta sanar da haka inda ta koka da yadda masu safarar mutane ke yin jigilar su zuwa kasashen waje da sunnan sama musu aikin yi a wadanna kasashe.

Sai dai kuma idan aka fita da su kuma sai su fada cikin mawucin hali da ba haka aka so ba. Wasu su kamu da cututtuka, wasu kuma ma har rasuwa suna yi.

Sakamakon binciken da hukumar dakile yaduwar cutar kanjamau ta kasa NACA ta yi ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 na dauke da kanjamau a Najeriya.

Idan ba a manta ba a watan Yuni ne Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa NAPTIP reshen jihar Kano ta cafke masu safaran mutane guda uku sannan sun ceto mutum 71 daga hannun su a jihar.

Hukumar ta yi wa masu safaran mutane diran mikiya bayan ta samu bayanan siri kan aiyyukan safarar mutane a jihar.

An Kama wadannan mutane yayin da suke hanyar zuwa kasashen Algeria, Morocco da Libya.

Share.

game da Author