Yadda Najeriya za ta iya farfado da tsarin ilmi – Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a yanzu akwai kananan yara sama da milyan 14 da ke gararamba, ba su shiga makaranta ba. Ya ce hakan tauye musu damar yin ilmi ne.

Sannan kuma ya ce tsarin ilmi a kasar nan ba zai taba gyaruwa ba,har sai matasa ne ke jan ragamar samar da ilmi a kasar nan.

Obasanjo ya yi wannan bayani a Lagos, lokacin da ya ke jawabi wurin taron Yaye Dalibai na “Teach for Nigeria Fellows”.

Kungiya ce da ta bada gudummawar bunkasa ilmin dalibai akalla 9,660 a makarantu 80 a jihohin Lagos, Ogun da Kaduna.

A wannan taron, an yaye dalibai 161 ne.

Kungiyar ta na maida hankali ne wajen kara bunkasa harkokin ilmi wadda wasu shugabanni a cikin al’umma suka maida hankalin aiwatarwa da gudanarwa.

Obasanjo ya ce, “wadannan milyoyin yara an tauye musu damar samun ilmin da za su iya yin amfani da basira da kwarewar su, ta yadda al’umma za ta amfana da su, kuma su ma su amfana da al’umma.

“Hujjoji na nuna cewa muddin ana so a gyara harkokin ilmi a kasar nan, to to sai matasa sun karbi ragamar kula da fannin ilmi.”

Ba a bangaren ilmi kadai ba, Obasanjo ya ce tilas sai matasa sun karbi jagorancin bangarori da fannoni da dsma a cikin al’umma, sannan za a iya fita daga kangin kalubalen da fannonin ilmi da sauran fannoni ke fuskanta a kasar nan.

“A na ku bangaren wannan kungiya, daliban su sun samu nasarar shiga gasanni daban-daban kuma su na cin nasara.

“Kwanan nan na samu labarin cewa daliban “Teach For Nigeria Fellows”, sun zo na biyu a Gasar ‘National Lafarge Comperition’ ta Kasa da kuma samun damar guraben karin karatu a makarantun gaba.”

Obasanjo ya shawarci su rika maida hankali wajen koya wa dalibai fasahai kirkire- kirkire domin kara wa ilmin su inganci da martaba.

Ya kuma nemi su zama wakilai na kwarai da kuma jakadun kawo canji mai nagarta da ‘yanci da adalci a Najeriya.

Obasanjo ya kuma yi tsokaci dangane da yadda cutar Coronavirus ta yi illa a kasashen Afrika.

Share.

game da Author