Yadda na yi mako uku cur ina kokuwa da Korona – Minista

0

Ministan harkokin Kasashen Waje Geoffrey Onyeama, ya bayyana yadda yayi fama da Korona har na tsawon makonni Uku.

Minista Onyeama ya ce abinda ya fi faranta masa rai shine yadda ma’aikatan jinya suka yi ta dawainiya da shi a lokacin da yake killace.

Sannan kuma ya jinjina wa ma’aikatan lafiya da kwamitin shugaban Kasa kan dakilae yaduwar cutar Korona, bisa kokarin da suka yi wajen wayar da kan mutane da ci gaba da himma wajen dakile yaduwar cutar a ksara nan.

” Kamuwa da Korona ba mutuwa bane. Idan ka kamu da ita sannan kaci gaba da shan magani kamar yadda kake yi wa wasu cututtukan zaka warke. Yana da kyau da zarar mutum yaji ba dadi a jiki ya gaggauta garzayawa asibiti a yi masa gwaji.

” Ni kai na bayan an yi mini gwaji, sai na fara shan maganin abinda ke damu na kafin a tabbatar da Korona ce. Na yi tsawon kwanki 21 a killace a ana dubani kuma cikin ikon Allah na war ke sarai yanzu.

Ina kira ga ‘yan Najeriya da aci gaba da kula da kai da kuma kiyaye dokokin hukuma NCDC domin tsare jiki daga kamuwa da cutar.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 453 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 113, FCT-72, Filato-59, Enugu-55, Kaduna-38, Ondo-32, Osun-26, Ebonyi-20, Ogun-9, Delta-8, Borno-7, Akwa Ibom-6, Oyo-5, Bauchi-1,, Kano-1 da Ekiti-1.

Yanzu mutum 47,743 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 33,943 sun warke, 956 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 13,512 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 16,188 FCT – 4,603, Oyo – 2,900, Edo – 2,399, Delta –1,621, Rivers 1,998, Kano –1,644, Ogun – 1,509, Kaduna – 1,729, Katsina –746, Ondo –1,359 , Borno –697, Gombe – 635, Bauchi – 579, Ebonyi – 967, Filato -1,667, Enugu – 1,069, Abia – 663, Imo – 486, Jigawa – 322, Kwara – 882, Bayelsa – 351, Nasarawa – 371, Osun – 678, Sokoto – 154, Niger – 226, Akwa Ibom – 251, Benue – 430, Adamawa – 199, Anambra – 156, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 196, Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 73.

Share.

game da Author