Yadda Manchester City ta yi rugurugu da Madrid

0

Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid ta tasha kashi a hannu Manchester City ta kasar Birtaniya a ci gaba da buga gasar wasan kwallon kafa na kungiyoyin nahiyar Turai wato ‘Champions League’

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga, Manchester City ta doke Madrid da ci 2-1 a can Madrid, a gaban dubban magoya bayanta.

An buga wannan wasa tun kafin barkewar annobar Korona.

A wasar ranar Juma’a kamar yadda Manchester City ta doke ta haka ta yi mata rugurugu a gida.

Sterling na Manchester City ya fara jefa kwallo a ragar Madrid minti 8 da fara wasa. A daidai minti 28 na cika cif sai Benzima na Madrid ya farke wannan kwallo. ya zama 1-1.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci kuma sai Jesus na Manchester ya jefa kwallo ta biyu a ragar Madrid. Haka dai madrid tayi ta fama har lokacin tashin wasa ya yi.

An dai tashi wasa 2-1 kamar yadda aka buga wasan farko a gidan Madrid. Manchester City ta lallasa Mardid da ci 4-2 kenan.

haka ita ma kungiyar Juventus ta sha kashi a hannun Lyon na kasar Faransa.

Share.

game da Author