Yadda Korona ta darkaki mutanen Afrika, Yanzu mutum sama da milyan daya suka kamu a Nahiyar

0

Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ta bayyana cewa mutum sama da miliyan daya sun kamu da cutar Korona a Afrika.

Yankin Afrika na daya daga cikin nahiyoyin da a duniyan korona ta yi wa mummunar kamu.

A yanzu dai kusan mutum miliyan 20 a kasashe sama 200 a duniya sun kamu da cutar.

An yi hasashen cewa lallai wannan cuta za ta yi wa yankin Afrika din mummunar Kamu saboda rashin ingantattun kiwon lafiya da kuma tsananin talauci da ake fama dashi a yankin.

Koma Bayan tattalin Arziki

Cutar Korona ta yadu zuwa kasashe 54 dake Nahiyar kuma mutane da dama sun rasa rayukan su sannan kasuwanci da na kai komo duk sun ruguje.

Binciken da tarayyar kasashen Afrika ta yi AU ya nuna cewa mutum miliyan 20 za su iya rasa aikin su a Afrika.

Sannan manya-manyan kasashen dake da arzikin man fetur kamar Najeriya da Angola za su yi asarar dala biliyan 65.

Domin guje wa irin haka ne gwamnatocin kasashen Afrika suka fara sassauta dokar hana walwala da aka saka domin dakile yaduwar a kasashen domin rage radadin talauci na Korona.

Sannan kuma akwai yiwuwar wasu da dama za su rasu, wasu kuma su kamu da ita kanta Korona din amma kuma basu sani ba.

Kasashen da suka fi fama da cutar covid-19 a Afrika.

Afrika ta Kudu

Mutum 553, 188.

Daga cikin Mutum miliyan 56 dake Zama a kasar Afrika ta Kudu gwamnativta Yi wa Mutum miliyan 3.2 gwajin cutar.

Masar

Mutum 95,000 ne suka kamu da cutar a Masar inda daga ciki Mutum 5,000 sun rasu.

Gwamnati ta yi wa mutum 135,000 gwajin cutar, daga cikin mutum sama da miliyan 100 dake Zama a kasan.

Najeriya

Adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 46577, Mutum 945 sun mutu bayan karin mutum 437 da kasar ta samu ranar Lahadi.

An i wa Mutum 317,496 gwajin cutar daga cikin’yan kasar mutum miliyan 200

Ghana

Kasar ta yi wa mutum kusan 410,000 gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 31 ‘yan kasar.

Ghana ce kasa ta farko da ta bude makarantu da kasuwani a Afrika.

Algeria

Sakamakon gwajin cutar coronavirus da aka fitar ranar Lahadi ya nuna cewa mutum 34,000 ne suka kamu da cutar, 1,200 sun mutu a kasar.

Gwamnati ta ce rashin kiyaye sharaddun guje wa kamuwa da cutar da mutane ke kin Yi na cikin dalilan da ya sa cutar barkewa a bangarorin kasan.

Haka kuma sauran Kasashen Afrika na fama da wannan cuta har yanzu, inda da yawa daga ciki duk sun sassauta dokar kulle domin a samu ci gaban walwala da rage radadin talauci da mutane fe fama da.

Share.

game da Author