Yadda Gwamnatin Buhari ta yafe wa wadanda suka shirya wa Babangida juyin-mulki

0

Majalisar Zartaswa a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bayyana sanarwar yafiya ga tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Bendel, Ambrose Alli.

Alli shi ne gwamnan mulkin farar-hula na farko na jihar, wadda ita ce daga baya aka datsa biyu, aka kirkiro jihohin Ondo da kuma Delta.

An kuma yafe wa wadanda suka shirya wa tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida juyin-mulki.

Marigayi Ambrose Alli dai a lokacin da ya na raye, an daure shi a wata barankyankyamar shari’a, saboda zargin ya danne naira 900,000.

Ministan Shari’a ya ce an yafe wa Ambrose Alli, saboda bayan an daure shi, ya biya kudaden da ake zargin ya danne.”

Bayan shi kuma akwai irin wasu tsoffin sojoji a yanzu, wadanda a lokacin su na aikin soja, suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Babangida.

Sun hada da Moses Effiong da E. J. Olarenwaju. Majalisar ta kuma yafe wa wani mai suna Ajayi Babalola.

Sannan kuma Malami ya shaida wa manema labarai cewa an yafe wa wasu daurarru su biyu, sai kuma wasu mutum 39 da aka yi wa sassucin dauri.

“Wannan kokari na daya daga cikin shirye-shiryen rage cunkoson gidajen kurkuku da wannan gwamnati ta sa a gaba.” Inji Malami.

“Kamar dai yadda ku ka sani, fiye da kashi 70 bisa 100 na daurarru da ake da su a gidajen kurkuku, duk masu jiran a yanke musu hukunci be. To saboda a rage cinkoso ne Shugaban Kasa ke wa wasu daurarrun afuwa, a bisa cancanta.”

Idan ba a manta ba, Buhari ya amince a rage yawan daurarrun da ke tsare a gidajen kurkukun kasar nan, a lokacin da cutar Coronavirus ta fara fantsama.

Ya ce a yi haka domin a rage cinkoso da kuma hana cutar Coronavirus yin illa a gidajen kurkuku.

Shugaba Muhammdu Buhari ne ke shugabancin wannan majalisa, dai Mataimakin sa, Yemi Osinbajo na tsimaka masa.

Majalisar ta na bada shawarwarin da suka dace ne ga Shugaba Buhari.

Ta kunshi dukkan tsoffin shugabannin kasa na farar hula da na soja, tsoffin Cif Jojin Najeriya, tsoffin shugabannin Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa. Tsoffin Gwamnoni da tsoffin Antoni Janar na Tarayya.

A taron da aka gudanar, rahotanni sun ce Olusegun Obasanjo ne kadai bai samu damar halarta ba, daga cikin tsoffin shugabannin Najeriya.

Share.

game da Author