Farashin abincin kaji da na kifi ya yi tashin-gwauron-zabo a kasar nan, makonni kadan bayan da Gwamnatin Tarayya a karkashin CBN ta soke lasisin shigo da masara daga waje.
Babban Bankin Najeriys, CBN ya bada sanarwar soke bada lasisi da kuma kudaden canji ga dillalan da ke shigo da masara daga kasashen waje.
Jama’a da dama sun ce wannan ya janyo hauhawar farashin abincin kaji da na kifin.
Wani binciken da PREMIUM TIMES ta yi a Abuja da Akwa Ibom, ya tabbatar da cewa farashin wata dusar kaji
mai suna ‘Starter’, wadda ake sayar da buhun ta mai nauyin kilo 25 kan naira 4,000, yanzu ya koma naira 4,200.
Shi ma wani abincin kaji da ake bai wa manyan kaji ba kanana ba, mai suna ‘finisher’, yanzu naira 4,000 ake sayarwa, maimakon naira 3,700 farashin sa a da.
Sai kuma wani abincin kifi wanda ake sayar da buhun sa naira 7,500, yanzu ya koma naira 8,100.
Wani abincin kananan kifi da ake sayar da buhun sa naira 6,300, yanzu naira 7,500 cur ake sayar da buhun sa. Duk kuwa da cewa kananan kifaye ne ake ciyarwa da abincin.
Akwai karamin buhu na naira 3, 900, yanzu naira 5,000 ake sayar da shi.
Dilallan abincin dabbobi irin su John Eze mai John Value Global Poultry and Fish da ke Akwa Ibom da kuma Linda Obutu mai Eljay Blessing Farm Limited, Kubwa, Abuja duk sun tabbatar da faruwar karin farashin abincin dabbobin. Kuma sun tabbatar cewa karin ya zama alakakai, kuma hana shigo da masara ya kawo karancin abincin dabbobin a kasuwa.
Shi kuwa Epriam cewa ya yi hana shigo da masara daga waje abu ne mai kyau, amma ba zai yi nasara ba, har sai gwamnati ta cika alkawurran bunkasa noma da ta yi wa manoman kasar nan tukunna.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda gwamnatin tarayya ta haramta shigo da masara, ta hanyar hana bai wa masu safarar ta daga waje. Kuma jaridar ta buga labarin yadda wani masani ya soki lamirin haana shigo da masara daga waje a wannan lokacin ya ce kuskure ne, zai durkusar da kiwon kaji a kasar nan.
An bayyana cewa hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke na hana shigo da masara daga kasashen waje, babban kuskure ne a wannan lokacin.
Daraktan Tsare-tsaren Bunkasa Harkokin Noma a Makarantar Nazarin Noma ta Lagos, Ikechukwu Kekikeme ne ya bayyana haka, tare da yin gargadin cewa wannan hukunci zai gurgunta harkokin kiwon kaji a kasar nan.
Ya ce a daidai wannan lokaci kusan kashi 50 bisa 100 na abincin kajin da ake samarwa a kasar nan, duk da masara ake hada su.
Ya ce to a yanzu masarar ta yi karanci, kakar samun wadatacciya bai zo ba, kuma a yanzu haka ta yi tsada, baya ga karancin da ta yi.
Duk da Kelikeme ya yaba tsare-tsaren CBN na bayar da lamunin noma, lamunin kanana da manyan masana’antu, to matsawar aka hana shigo da masara a yanzu, dimbin manoman da suka bada himma wajen kiwon kaji za su yi asara, harkokin su za su gurgunce.
Daga nan ya kara da cewa ana hana shigo da masara, to fa duk wani kokari da CBN ya yi domin bunkasa harkokin noma zai tarwatse baki daya.
Ya bayar da shawarar gwamnati ta gaggauta shigo da masara domin kada nan da ‘yan watanni matsalar da ake fuskanta ta karancin masarar ta rubanya yadda ake ciki a yanzu.
Kelikeme ya ce nan gaba gwamnati ta sake nazarin lokacin da ya fi dacewa ta hana shigo da masara. Amma dai hana shigo da ita a yanzu, dabarar-rashin-dabara ce.
A makon jiya ne dai PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya datakar da shigo da masara daga waje.
Hakan ya faru ne bayan da manoma suka yi kakkausan korafin ana ci gaba da shigo da metrik tan 400,000 duk shekara a jere tsawon shekaru biyu.
Kwana day bya bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa har yanzu shekaru biyu a jere tulin masarar da Najeriya ke shigowa da ita kasar nan bai ragu ba, duk da korafin da manoma ke yi cewa za su iya noma masarar da za a ci kuma a yi abincin dabbobi da ita, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana dakatar da shigo da masara daga wajen Najeriya.
CBN ya dakatar da shigo da tulin masarar ce ta hanyar bayyana daina bayar da canjin musayar kudaden waje ga masu sayo masara daga kasahen ketare.
CBN ya yi wannan sanarwar gaggawa ce ta hannun O. S. Nnaji, Darakta Ciniki da Musayar Kudade.
Ya ce an dauki matakin ne domin a bunkasa noman masara a nan cikin Najeriya.
“Domin kokarin mu na bunkasa noman masara a kasar nan da bunkasa tattalin arzikin kasa, farfado da tattalin arziki, kare hanyoyin cin abincin al’ummar karkara da kuma kara samar da aikin yi sakamakon kuncin da cutar Coronavirus ya haddasa, ana sanar da halastattun dillalan masara su dakatar da neman musayar kudaden shigo da masara cikin kasar nan, daga yanzu.” Cewar sanarwar.
CBN ta ce ta dakatar da bayar da musayar kudade a Matakin Form M. Wannan kuwa shi ne daftarin bayanan kayan abincin da ake shigowa da shi, wanda CBN da shi ta ke sa-ido kan kayan da aka shigo da shi. Kuma ta hanyar ‘Form M’ ake karbar harajin kayan da aka shigo da su kasar nan.
Amma kuma CBN ya umarci dilolin su damka mata fam-fam din da suka rigaya suka cike. Za a rufe karba a ranar Laraba, 15 Ga Yuli, 2020. Inji sanarwar.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cewa, kukan da manoma ke yi cewa a daina shigo da masara bai sa gwamnati ta hana shigo da ita ba, domin bayanan
Hukumar Bunkasa Harkokin Noma ta Amurka, ta ce a cikin 2019 Najeriya ta shigo da masara daga waje, adadin da rabon da ta shigo da shi tun cikin 2009.
USDA ta ce Najeriya ta shigo da tan na masara har 400,000 a cikin 2019, daidai abin da ta shigo da shi a baya cikin shekarar 2009.
Rahoton ya ce tan 400,000 din su ne na biyu a yawan masarar da Najeriya ta shigo da ita, tun shekarar 2016 da ta shigo da tan 650,000 na masara.
Masara ta zama daya daga cikin manyan kayan abinci a Afrika, tun bayan shigo a ita a nahiyar a cikin shekarun 1500s.
Najeriya ce kasar da ta fi kowace kasa noman masara a Afrika. Daga ita sai Tanzania, kamar yadda Cibiyar Binciken Noma a Afrika ta tabbatar.
Sai dai kuma abin mamaki, duk da haka Najeriya kuma it’s ce ta fi kowace kasa a Afrika shigo da masara a fadin Afrika.
Hakan ya na faruwa ne saboda yadda bukatar abincin dabbobi ke karuwa a Najeriya.
A duk shekara na bukatar metrik tan milyan 15 na masara. Amma kuma ta na noma metrik tan milyan 10.5 kadai.
Shekaru da dama manoman masara a Najeriya na korafin cewa za su iya wadatar da kasar nan masarar da ake ci da kuma wadda ake ciyar da dabbobi baki daya.
Dalili kenan manoman masara ke korafin cewa Najeriya ta ki hana shigo da masara kamar yadda ta haramta shigo da shinkafa.
Edwin Uche, Shugaban Kungiyar Manoma da Machasa Shinkafa na Kasa, MAGPAN, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa “idan gwamnati ta tallafa mana ta ba mu goyon baya, za mu iya noma masarar da za a ci a kasar nan, har wadda za a yi amincin dabbobi da ita.”
Najeriya ce ta uku a jerin kasashen da suka sayo masara daga waje. Zimbabwe ce ta farko, wadda ta sayo tan milyan 1, sai Kenya ta 2 da ta sayo tan 900,000.
A nan Najeriya, Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin tallafa wa manoman masara 200,000 a fadin kasar nan.
A cikin watan Yuni CBN ya bayyana haka, lokacin da aka kaddamar da shirin noman masara na daminar bana a Jihar Delta.
Yayin da CBN ta dakatar da shigo da masarar, ta bayyana cewa za ta rubanya kudaden tallafin noman masara da za ta bayar da dimbin manoma a wannan shekarar, matsawar ta ga cewa sun sa himma sosai wajen wadatar da kasar nan da wadatacciyar masara.