Takardun bayanai da rekod-rekod na Kotun Ingila sun kara nunawa da tabbatar da cewa kotun ta zartas wa Shugaban Kamfanin Rahamaniyya, Abdulrahman Bashir dauri a kurkuku. Sai dai kuma babban mai hada-hadar fetur din ya turo wa PREMIUM TIMES bayanin cewa ba gaskiya ba ne labarin da ta buga a kan sa.
Wannan jarida ta buga labarin cewa Kotun Ingila ta daure mai Rahamaniyya Oil.
Kotun Ingila ta yanke wa Abdulrahman Bashir, Shugaban Rahamaniyya Oil daurin watanni 10 a gidan kurkuku.
Cikin watan Fabrairu ne Mai Shari’a Butcher na Babbar Kotun Ingila da Wales ya yanke hukuncin dauri a kan mai Rahamaniyya saboda kotu ta same shi da laifin raina kotu da karya umarnin kotu ba sau daya ba ya yi, a wata shari’a da kamfanin mai na Sahara Energy Resources Ltd su ka maka kara a kotun.
Yadda Rahamaniyya Ya Ja Wa Kan Sa Dauri A Kurkuku:
“Makasudin wannan hukuncin daurin da aka yi wa Abdulrahman Bashir, saboda:
1. Ya bijire wa umarnin Mai Shari’a Robin Knowles ya bayar a kan sa a ranar 1 Ga Agusta, 2019.
2. Ya kangare wa umarnin da Mai Shari’a Bryan ya bayar a kan sa, a ranar 6 Ga Satumba,2019.” Haka alkalin da ya yanke masa wannan hukuncin daurin ya bayyana.
Me Kotu Ta Ce Ya Yi Amma Ya Ki Yi, Har Ta Daure Shi?:
Kotu ta bada umarnin cewa mai Rahamaniyya Oil and Gas bai wa kamfanin Sahara Energy Resources Ltd metrik tan 6,400.69 na man gas.
Kotu ta nemi Abdulrahman Bashir ya sa kamfanin sa Rahamaniyya Oil and Gas ya bada wannan lodin dimbin mai tashar lodin jirage masu jigilar mai ta bakin ruwan Kirikiri, Apapa da ke Lagos.
Bashir ya karya wannn umarni ta hanyar kasa bai wa kamfanin sa Rahamaniyya Oil and Gas umarnin bada man gas din ga Sahara Energy, a tashar jiragen ruwa ta Apapa.
Yanzu haka PREMIUM TIMES HAUSA ta mallaki kwafe-kwafen takardun shari’a da hukuncin daurin da aka yi wa mai Rahamaniyya.
Har ila yau, cikin hukuncin da kotun ta yanke, Mai Shari’a ya ce za a iya sassauta masa zaman kurkuku zuwa watanni shida, idan ya bi unarnin da kotu ta gindaya masa, har ya bada adadin man gas din da kotu ta ce ya bai wa Sahara Energy.
Mai Rahamaniyya Ya Ce Ba A Yanke Masa Hukuncin Dauri A Kotun Birtaniya Ba:
Cikin wata takarda da kamfanin ya aiko wa PREMIUM TIMES a ranar Asabar, ya amince sun yi hada-hada da kuma yarjejeniya da Sahara Energy Resources Ltd. Amma ya ce wata kotu ba ta daure shi ba.
Cewa kamfanin ya yi wannan labari ya bai wa Abdulrahman Bashir mamaki da al’ajabi.
Ya Warware Tankiyar Hukuncin Dauri: Babban Daraktan kamfanin, Awosika, daga bisani ya sanar wa PREMIUM TIMES cewa akwai hukuncin daurin kotun Birtaniya a kan mai Rahamaniyya Oil and Gas, da kuma kwantacciyar shari’ar da ya ke tafkawa da kamfanin Sahara Energy Resources Ltd.
Sai dai kuma ya ce lauyoyin sa ne suka shi Abdulrahman din shawara, fatawa da karin haske cewa waccan kotu ta Ingila ba ta da hurumin da za ta iya daure shi, domin batun da ake tankiya a kai, batu ne da ya faru a Najeriya ba a Ingila ko karkashin Birtaniya ba.
Ya ce akwai yarjejeniya cewa za a biya kudin cikin Disamba, amma saboda tsayawa cak da komai ya yi a duniya saboda barkewar cutar Coronavirus, hakan bai yiwu ba.
Ya ce a cikin watan Yuni da Yuli, Abdulrahman Bashir mai Rahamaniyya ya biya Sahara Energy Resources Ltd, dala milyan 1.4.
“Yarjejeniya ce aka kulla a cikin watan Yuni, inda Sahara Energy Resources Ltd ya ce idan aka biya shi kudin sa, to zai koma Kotun Birtaniya ya ce kamfanin Rahamaniya ya biya shi abin sa.”
Sai dai Awosika ya ce ba zai iya bai wa PREMIUM TIMES shaidar rasidin biyan dala milyan 1.4 ga Sahara Energy Resources Ltd ba, saboda ba shi da iznin yin haka.
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin manyan jami’an kamfanin Sahara Energy Resources Ltd., amma sun ki daukar waya, kuma sun ki maida amsar tambayoyin da aka yi masu ta sakonnin tes.