WATA SABUWA: ‘Yan Al-Qida sun kwararo yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya – Sojan Amurka

0

Wani Kwamanda a rundunar sojojin kasar Amurka Dagvin Anderson da ke aiki a yankin Afrika ya gargadi gwamnatin Najeriya cewa kungiyoyi irin su Al-Qida na kwararowa yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.

” Yanzu haka suna samun matsuguni da gudanar da ayyukansu a yankin Arewa Maso Gabas, Musamman yankunan Barno. Yanzu kuma sun fara kafa sansanoni a yankin Arewa Maso Yamma, a Najeriya.

Jihohin Arewa Maso Yamma sun hada da, Kaduna, Kano, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina da Jigawa.

” Zamu hada kai da Najeriya domin mu rika sanar da juna bayanan sirri game da yadda wadannan kungiyoyi ke kokarin mamaye Najeriya. Kungiyoyi kamar su Al-Qida, Boko Haran, ISIS, da ISWAP. Za mu rika raba bayanan sirri a tsakanin mu domin sanin yadda za a tunkare su.

” Babu wata kasa da zata zo ta yi wa Najeriya yaki. Dole dai ita ce zata yi wa kanta abinda ya dace ko, Kasar Amurka, Britaniya, da wasu kasashe na Turai duk dai sai dai su taimaka mata amma ita ce wuka ita ce nama a wannan aiki.

” Dole sai mun fahimci mene Najeriya ke so mu taimaka mata da shi. Daganan sai gaba dayan mu mu ko mu tsara yadda za mu tsara abubuwan.

” Najeriya shirgegiyar kasa ce, daje da iyakoki da kasashe a zagaye da ita. Dole ta maida hankali wajen yin amfani da jiragen yaki na sama idan tana so da iya dakile hare-hre da kwararan ‘yan kungiyoyi haka.

Share.

game da Author