WAEC: Dalibai 20 masu rubuta jarabawa sun kamu da Korona

0

A ranar Alhamis ne babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Bayelsa Inodu Apoku ya bayyana cewa dalibai 20 dake rubuta jarabawar karshe na babban sakandare WAEC a jihar sun kamu da cutar Korona.

Wannan sanarwa da ma’aikatar kiwon lafiya ta fitar ya zo kwanaki uku da gwamnan jihar Akwa-Ibom Udom Emmanuel ya sanar cewa wani dalibi dake rubuta jarabawar WAEC ya kamu da cutar a jihar.

Udom bai fadi sunan dalibin ba ko makarantar da dalibin ke rubuta jarabawar ba.

Bayan haka jaridar ‘Punch’ ta bada labarin yadda kwamishinan kiwon lafiya na jihar Gombe Habu Dahiru ya sanar cewa jihar ta kara samun dalibi guda daya da ya kamu da cutar Korona yayin da ake zana jarabawar WAEC ranar Laraba.

Zuwa yanzu dalibai 8 ne Suka Kamu da cutar a jihar.

Idan ba a manta ba a watan Yuli ne Ma’aikatan ilmi na Najeriya ta bayyana cewa za a zana darusan jarabawar WAEC da ake yi a Najeriya ranar 5 zuwa 14 ga watan Satumbar 2020.

Gwamnati ta kuma ce sauran darusan jarabawan da ake yi a kasashen Afrika ta yamma da suka hada da Najeriya, Ghana, Sierra Leone da Gambia za a zana su ranar 17 ga Agusta.

Karamin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ya sanar da haka ranar Litini a taron da Kwamitin Shugaban Kasa Kan dakile yaduwar cutar Korona da tayi a Abuja.

Share.

game da Author