Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa tulin basussukan da Najeriya ta ciwo daga kasar Chana, ba zai kumbura wa kasar nan ciki har ya fashe ba.
Amaechi ya ce Najeriya na da karfin biyan basussukan da aka ciwo daga Chana a cikin shekaru 20, kamar yadda yarjejeniyar karbar bashin da bayar da bashin ta ke a rubuce.
Cikin wata sanarwar da Minista Amaechi ya fitar a ranar Asabar, ya ce ya kamata jama’a su fahimta cewa a wannan zamani da duniya ke ciki, Chana ce kadai za ta iya bada bashi tare da dora kudin ruwa kashi 2.8 kacal na uwar kudin da aka karba lamunin.
“Kuma babu wata kasar da za ta bada lamuni haka kai-tsaye ba tare da an ajiye garanto ba, sai Chana.”
Ya ce shi yarjejeniyar cinikayya ce ma’aikatar sa ke sa wa hannu, kamar tsakanin Gwamnatin Tarayya da wani kamfani.
“Amma yarjejeniyar karbar lamuni tsakanin kasa da kasa, wato Najeriya da kasar Chana, to wannan kuma Ma’aikatar Harkokin Kudade ce ke a sannu a madadin Najeriya.”
Amaechi ya ce ana ciwo basussukan ne domin a kammala aikin titinan jiragen kasa.
“Maganar gaskiya dai ita ce, a yanzu idan ba Chana ba, babu wanda zai kwashi makudan kudade haka siddan ya bayar lamuni, ba tare da wasu sharudda ko yarjejeniya a tsakanin ta da mai karbar lamunin ba.
“A cikin yarjejeniyar akwai Sharadi Na 8: A nan, mai bada lamuni zai zo neman bashin sa idan har ba a kammala biya kafin ranar da wa’adin biya ya cika ba. To da ka zo da wani zance daban, za ta ce ai ba ka da wata kariya ko uzuri kuma.”
Cikin 2017 dai Najeriya ta karbo bashin dala bilyan 7.5 domin aikin gina titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Kano.
An kuma karbo dala bilyan 1.5 domin aikin titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan.
Cikin 2020 kuma Majalisar Dattawa ta amince a karbo lamunin dala bilyan 22 daga Chana, lamunin da Shugaba Muhammdu Buhari ya roke su a rubuce su amince ya ciwo.
Ko da ya ke dai an tabbatar da cewa dala bilyan 17.5 ne za a karbo a Chana daga cikin kudaden a EXIM Bank da ke Chana.
Amaechi ya ce tuni Najeriya ta fara biyan wasu basussukan.
“Akwai ma wasu bashi na dala milyan 500 da Gwamnatin Goodlluck Jonathan ta ciwo, wadanda an fara biyan naira milyan 96.
“Sannan kuma ina so jama’a su gane cewa duk wani bashi da aka ciwo, sai da amincewar Majalisar Dattawa da ta Tarayya.
“Babu kasar da za ta bada bashi ba tare da ta ga sa hannun amincewar Majalisar kasar da ke neman bashin ba.” Inji Amaechi.