TITIN ABUJA ZUWA KANO: Ƴan Majalisa sun damu da yadda aikin ke yin tafiyar-kunkuru

0

Mambobin Majalisar Tarayya sun nuna matukar damuwa dangane da yadda aikin gyaran titin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano ke tafiyar-hawainiya, ko tafiyar-kunkuru.

Tun cikin 2018 aka bayar da kwangilar aikin, amma ga shi har 2020 ta kusa shuɗewa, ba a yi nisa da aikin ba.

Shugaban Kwamitin Ayyuka Honarabul Kabir Bichi, daga Jihar Kano, shi ne ya nuna wannan damuwa a lokacin da ya kai wa Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ziyara a ranar Juma’a.

Bichi ya ce sun kai ziyara Kano a matsayin ziyarar duba yadda ayyukan gyaran titin ke tafiya, wanda ko kadan ba su gamsu da irin jan-kafar da ake yi wa aikin ba.

Dan Majalisar ya ce a gaskiya kamfanin gina titina na Julius Berger ya ba su kunya, ganin yadda a tsawon shekaru sama da biyu aikin da ya yi bai taka kara ya karya ba.

Ya ce kusan akwai bukatar gaggawa kwamitin su ya shawarci gwamnatin tarayya ta rarraba aikin titin mai tsawon kilomita 400 ga wasu kamfanoni, wadanda za su taya Julius Berger kammala aikin da sauri a kan lokaci.

“Ba mu ji dadin yadda tun fara aikin watanni 26 da suka gabata ba, amma a ce har yau aikin da aka yi bai ma kai kashi 20% bisa 100% ba.

“Duk da cewa sun karbi naira bilyan 70 daga cikin naira bilyan 155 na yawan kudin kwangilar, har yanzu ba su yi abin kirki ba. Amma kuma a ka’ida, watanni 36 suka diba, suka ce a cikin su za su kammala aikin gaba daya. Go ga shi yanzu an ci watanni 26, saura watanni 10 kacal suka rage.

“A bangaren farko na aikin daga Zuba zuwa Kaduna, abin haushi da takaici, aikin kilomita 10 kadai aka yi. Amma fa nisan kilomita 165 ne daga Zuba zuwa Kaduna.

“Gyaran da aka yi daga Kaduna zuwa Zaria bai fi na tsawon kilomita biyar zuwa shida ba. Kuma daga Zaria zuwa Kaduna nisan kilomita 75 ne.” Inji Hon. Bichi.

Ya kara da cewa Majalisar Tarayya ba za ta amince da kara wa masu kwangilar gyaran titin wa’adin kammala aikin su ba.

Ya ce saboda rashin kammala aikin da wuri sai asarar rayuka da dukiyoyi ake ta yi ba kakkautawa a kan titin.

Ya kara da cewa a irin yadda aikin ke tafiya, babu yadda za a yi Shugaba Muhammadu Buhari ya bude titin kafin ya kammala zangon sa na biyu.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda aikin titin Kano zuwa Maiduguri ya ki ci, ya ci cinyewa, tsawon shekaru 10 kenan.

Share.

game da Author