Tattalin arzikin Najeriya bai shiga garari kamar yadda Hukumar NBS ta bada rahoto ba – Fadar Shugaban Kasa

0

Duk da cewa Karfin Tattalin Arzikin Najeriya ya rika tsfiya da giyar ribas tun daga watan Afrilu zuwa Yuni, 2020, Fadar Shugaban Kasa ta ce a haka din ya fi na wasu manyan kasashen duniya bunkasa a wancan tsukun lokacin.

Haka dai sanarwar da fadar ta fitar a ranar Laraba.

Ranar Talatar da ta gabata ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa tattalin arzikin Najeriya na ci gaban mai ginin rijiya.

Tattalin Arzikin Cikin Gida na Najeriya (GDP) ta kakare tare da yin tafiyar-kura, abin da aka fi sani da ci gaban mai ginin rijiya, a tsakanin watannin Afrilu, Mayu da Yuni na shekarar 2020.

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), mallakar gwamnatin tarayya ce ta bayyana haka a ranar Litinin cewa tattalin arzikin ya tafi da baya-baya har da kashi -6.1%

Rahoton Bayanan Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) na watannin Afrilu, Mayu da Yuni (Q2 2020), ya nuna cewa saboda tsayawa cak da harkokin cinikayyar kasa da kasa da zirga-zirgar cikin kasashe a lokacin zaman gida tilas saboda cutar Coronavirus, tsakanin Afrilu zuwa karshen Yuni, tattalin arzikin ya shiga jula-jula.

An dai rufe hada-hadar komai da komai a kasashen duniya saboda barkewar annobar Korona a cikin watannin uku.

Najeriya ta kulle komai da komai, tun daga harkokin gwamnatin tarayya, makarantu, kasuwanci, zirga-zirga, masallatai da coci-coci saboda Coronavirus.

NBS ta lura a ranar Litinin cewa wadancan tsauraran matakan da aka gindaya na hana zirga-zirga ne suka haddasa tattalin arzikin xi gida na Najeriya ya rika yin tukin baya-da-baya.

Wannan jula-jula da tattalin arziki ya shiga, ya kawo karshen bunkasar da ake gani ya dan yi cikin shekaru uku,tun bayan kuncin tattalin arzikin da Najeriya ta shiga cikin 2016.

PREMIUM TIMES ta buga labari a cikin makon da ya gabata cewa sama da mutum milyan 50 a Najeriya ba su day cin yau balle na gobe.

A karshen makon nan kuma jaridar Punch ta buga labarin cewa kashi 61 zuwa 63 bisa 100 na ‘yan Najeriya a sayen abincin yau da gobe ‘yan kudaden da suke samu ke tafiya.

Raddin Fadar Shugaban Kasa:

“Duk da tafiyar baya-baya da NBS ta ce karfin tattalin arzikin Najeriya ya yi, fadar shugaban kasa ta ce a hakan ma ya yi karfin juriyar fiye da alkaluman da masana da dama suka yi kintacen zai yi kasa ba.

Fadar ta ce, “A haka din tattalin arzikin Najeriya ya kara bunkasa a watannin uku, fiye ma da na Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus, Italy, Canada, Japan, Afrika ta Kudu.

Kakakin Yada Labarai Femi Adesina ya kara da cewa Chana kadai ce kasar da tattalin ta ya haura sama da kashi +3%.

“Na Amurka ya ragu da -38%, na Faransa -14 %, na Jamus ma -10 da sauran su ”

Sanarwar ta ce dama gwamnatin tarayya na sane da hakin matsin da ake ciki da kuma wanda za a shiga a lokacin, saboda barkewar cutar Coronavirus.

Daliki kenan gwamnatin tarayya din ta rika bayar da tallafi daban daban domin rage wa ‘ysn Najeriya radadin halin kuncin da aka shiga.

Share.

game da Author