SULTAN: Abinda muka tattauna da Sarkin musulmi a fadar gwamnati – El-Rufai

0

Mai martaba Sarkin Musulmi ya ziyarci gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a fadar gwamnatin jihar dake Kaduna ranar litini.

Duk da cewa sun yi ganawa a asirce ne, gwamnan Kaduna ya bayyana wa manema Labarai cewa sarkin Musulmi ya yi masa ziyarar zumunci ne.

” Sarkin Musulmi wana ne domin tun a makarantar Sakandare da mukayi a Zariya, wato Barewa College, yana gaba da mu.

Bugu da kari ya ce ya garzayo Kaduna ne domin shima ya gani kuma ya ji wa kan sa daga bakin gwamnan abubuwan da ke faruwa a jihar.

” Sannan kuma ya yaba wa kungiyoyin da basu ga maciji a tsakanin su, suka hadu domin yin sulhu da neman su zauna lafiya a tsakanin su. A karshe ya yi addu’ar Allah zaunar da jihar Kaduna Lafiya da kasa baki daya.

El-Rufai ya kara da cewa sun tattauna bau da dama da sarkin musulmin sai dai kuma wannan tsakanin su ba na gama gari bane.

Idan ba a manta ba tun a litinin makon jiya ne gwamna El-Rufai ya ke ta karbar baki a fadar gwamnatin jihar. Baya ga shugaban kungiyar Kiristoci da ya ziyarce shi, tsohon Sarkin Kano kuma aminin sa Sanusi Lamido shima ya ziyarce shi ranar Lahadi.

Gaba dayan su sun yi kira ga mutanen Kaduna da su zauna lafiya da kuma fatan Allah ya kawo karshen rashin zaman lafiya da ake fama da shi a kasar nan.

Share.

game da Author