Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana a wata takarda da kakakin sa Muyiwa Adekeye ya saka wa hannu cewa dama bashi ne ya nemi sai an saka shi cikin wadanda za su yi jawabai a taron kungiyar lauyoyi da za a yi a makon gobe ba.
El-Rufai ya ce wannan taro da ma gayyatar sa shugabannin kungiyar suka yi sannan suka bashi damar zai yi jawabi kan ingancin zama dan kasa.
” Ko da kungiyar NBA ko babu magana dai ba hana shi za ayi ba. Zai ci gaba da tofa albarkacin bakin sa akan duk abin da zai kawo hadin kai da cigaban Najeriya.
” Abin da shugabannin kungiyar NBA suka yi bai dace ba ace wai za su saurari bangare daya ne kawai banda wani bangaren. Idan an ce ga wani abu akan mutum ay sai su nemi ji ta bakin wancan mutumin shima a matsayin su alkalai.
Sannan kuma maganan tsaro a Kaduna, gwamna El-Rufai yayi abinda ba a taba yi ba shekaru 40 da ake ta fadi tashi game da rashin zaman lafiya a yankin Kudancin Kaduna.
Kuma dai ay ba yankin bane kawai ake kashe-kashe a jihar, saboda wadanda suke ganin su shafaffu da mai ne suna da ikon shiga jaridu da masu mara musu. Sai su kadai ake fadi ba za a zo a ga sannan a tantance ainihin abinda ke faruwa ba domin su wasu basu da bakin magana. Shi dai kokarin sa shine kowa a kare shi a kuma bi wa kowa hakkin sa.
Sannan kuma gwamna Nasiru ne gwamnan na farko da ya kafa sansanonin sojoji da na ‘yan sanda a yankin Kudancin Kaduna. Sannan ya fafa kwamitoci domin a samu zaman lafiya a jihar.
Wadanda suke ganin cewa jihar Kaduna ce jihar da ta fi fama da rashin zaman lafiya a yankin Arewa Maso Yamma, sai su ci gaba da mafarkin su shi dai gwamna El-Rufai ya san abinda ya ke yi kuma zai ci gaba da haka domin zaman lafiyar mutanen jihar.
Kungiyar Lauyoyi Ta Cire Sunan El-Rufai Daga Wadanda Zasu Yi Jawabi A Taron Kungiyar
Bayan nuna rashin amincewarsu da daruruwan Lauyoyin Kasar nan suka yi cewa basu amince gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya halarci babban taron kungiyar na shekara-shekara ba, kungiyar ta cire sunan gwamnan cikin jerin manyan kasar nan da za su yi jawabi a wannan taro.
Sakataren yada labaran kungiyar, Kunle Edun ya shaida wa PREMIUM TIMES kai tsaye cewa, bayan korafin da suka samu daga daruruwan mambobin su, kwamitin gudanarwar kungiyar ta janye halartar gwamna El-Rufai wannan taron shekara-shekara na Kungiyar.
Edun yace za a sanar da gwamna El-Rufai game da wannan matsaya na Kungiyar.
Dalilan da yasa mambobin kungiyar lauyoyi suke adawa da gayyatar El-Rufai taron Kungiyar
Lauyoyin Najeriya masu tarin yawa sun rubuta sunayen su a wata rajistar wadanda ba su yarda Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya halarci gagarimin taron su na kasa, na shekara-shekara ba.
Tun da farko dai gwamnan ya na cikin wadanda Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) ta gayyata a matsayin Bakon Na Musamman Mai Jawabi, a taron wanda za a yi daga ranar 26 zuwa 29 Ga Agusta.
Manyan masu jawabai na musamman za su yi gurugubjin tattaunawa ne a kan: “Wane Ne Dan Najeriya?” Wato wata gogayyar wasa kwakwalce aka shirya yi a kwanaki ukun taron a kan tabbatar zama cikakken dan Najeriya.
Sauran wadanda za su yi jawabi a wudmrin har da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Gwamna Nyesom Wike na Ribas, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila da Cif Jiojin Najeriya, Tanko Muhammad.
Akwai Olusegun Obasanjo da Ministan Shari’a, Abubakar Malami da sauran su.
Wannan ne taro na shekara-shekara na 60 da Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta shirya.