Soke Jam’iyyu: INEC Za Ta Je Kotun Koli Kan Sabanin Hukunci

0

Hukumar Zabe mai Cin Gashin Kan ta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta shigar da kara a Kotun Koli saboda hukunce-hukunce biyu masu karo da juna wadanda Kotun Daukaka kara ta yanke a kan soke rajistar jam’iyyu.

Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin
yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a ranar Litinin.

A cikin sanarwa ga manema labarai da ya fitar mai taken, “Hukuncin Kotun Daukaka Kara: INEC Za Ta Tuntubi Kotun Ƙoli,” Okoye ya ce: “Hukumar Zabe Mai Cin Gashin Kan ta ta Kasa (INEC) ta karbi hukuncin da Kotun Daukaka Ƙara ta kawo mata a yau, 10 ga Agusta, 2020 game da daukaka karar da jam’iyyar ACD da wasu 22 su ka shigar a kan soke su da wannan Hukuma ta yi.

“A hukuncin da Kotun Daukaka Karar ta yanke, kotun ta ce soke jam’iyyar ACD da wasu 22 da aka yi ya saba wa ƙarfin Hukumar kuma ta umurci Hukumar da ta sake dawo da su.

“Idan mun tuna, tun a ranar 29 ga Yuli 2020 ne Kotun Daukaka Karar, Yankin Shari’a na Abuja, a wani daukaka kara da jam’iyyar National Unity Party (NUP) ta kai, ta tabbatar da ikon Hukumar (INEC) na soke jam’iyyun da su ka gaza cika tanade-tanaden da ke cikin sashen tsarin mulki mai lamba 225A. Lokacin da jam’iyyar National Unity Party ba ta gamsu da hukuncin ba, sai ta ɗaukaka ƙara wanda har yanzu maganar ta na gaban Kotun Koli.”

Okoye ya kara da cewa, “Saboda haka dai yanzu Hukumar na fuskantar hukunce-hukunce guda biyu masu karo da juna daga Kotun Daukaka Ƙara; daya na tabbatar da hurumin Hukumar na soke rajistar jam’iyyu, sannan dayan na rusa soke rajistar ACD da wasu 22 da aka yi.

“Tunda an kawo hukunce-hukunce guda biyu da su ka saɓa wa juna, kuma daga kotu daya, yanzu Hukumar ba ta san wanne za ta ɗauka ta yi aiki da shi ba ta bar dayan.

“Sakamakon haka, Hukumar za ta je Kotun Ƙoli domin a yanke hukuncin karshe kan lamarin wanda ya samu a sanadiyyar hukunce-hukuncen guda biyu.”

Ya ce a yanzu dai “Hukumar ta dukufa ne kan shirye-shiryen da ta ke yi don gudanar da zabubbukan gwamnonin jihohin Edo da Ogun waɗanda aka shirya yi a ranakun 19 ga Satumba, 2020 da 10 ga Oktoba, 2020, kuma ta na bin jadawalin ranakun yin zabubbukan tiryan-tiryan kamar yadda Tsarin Mulki da Dokar Zabe su ka gindiya mata.

“Mu na tabbatar wa da ‘yan Nijeriya, musamman ma mutanen jihohin Edo da Ondo, cewa Hukumar ta na nan a kan bakan ta wajen aiwatar da aikin ta yadda ya kamata.”

Share.

game da Author