Sojoji sun kashe mahara uku, sun ceto mutum 10 a jihohin Katsina da Zamfara

0

Dakarun sojin Najeriya dake karkashin rundunar ‘Operation Sahel Sanity’ sun kashe mahara uku, sun cafke wasu maharan 10 sannan sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara.

Mataimakin Shugaban yada labarai na rundunar Benard Onyeuko ya Sanar da haka ranar Alhamis a garin Katsina.

” A ranar 16 ga watan Agusta dakarun sun gudanar da bincike a wasu maboyar maharan dake dajin Dumburum.

“A nan ne fa aka cafke maharan guda uku, bindiga daya da harsashen bindigan da dama.

Onyeuko ya ce dakarun sun kukkutsa cikin dajin dake kewaye da jihohin Katsina da Zamfara tun daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Agusta.

Bagaga, Yarmalamai, Munhaye, Bena, Unguwar-tsamiya, Unguwar-Malama-Rama, Yadi da Tudun-Ali na daga cikin dazukan da dakarun suka kukkutsa.

Dakarun sun ceto Mutum 19 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Idan ba a manta ba a wannan mako ne kodinatan yada labarai na Ma’aikatar Tsaron Najeriya, John Enenche ya ce dakarun sojoji dake karkashin ‘Operation Lafiya Dole’ sun kashe ‘yan ta’adda da dama a kauyen Tashan Kare dake jihar Niger.

Enenche ya bayyana cewa dakarun sun yi amfani da bayanan sirri game da ayyukan wadannan mahara.

” Daga nan ne fa aka gaggauta tura sojoji inda suka yi arangama da wadannan ‘yan ta’adda suka kashe na kashewa wasu kuma suka arce.

Sai dai Kuma sojoji biyar sun ji rauni a wannan bata kashi.

Enenche ya ce hakan da dakarun suka yi na daga cikin gagarimin shirin kakkabe ta’addanci baki daya da ake yi a yankin Arewa ta Tsakiya.

Share.

game da Author