Sojoji 3, Boko Haram 8 suka rasa rayukan su a arangamar Kukawa – Rundar Sojojin Najeriya

0

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa sojoji 3 da Boko Haram 8 ne aka rasa a arangamar da sojoji da Boko Haram suka yi a garin Kukawa sannan wasu Boko Haram din sun gudu da raunin harsashi a jikinsu.

Harin ranar Talata a garin Kukawa ya auku ne a lokacin da mazaunan garin ke komowa bayan sun dauki tsawon shekaru biyu a sansanin ‘yan gudun hijra.

Wani mazaunin garin Ali Gonimi ya bayyana cewa maharan da suka far wa garin na sanye da kayan sojoji ne.

“Ko da muka hango su suna zuwa mun yi zatin sojojin Najeriya domin suna sanye da kayan sojoji. Abin da ya bambamta da sojojin shine suna rike da bakin tuta dake dauke da rubutun arabi a ajiki.

“Da suka shigo garin sun shaida mana cewa ba za su kashe kowa ba sai dai idan suka fara artabu da sojojin Najeriya, kowa ya kama gaban sa kawai.

Wani cikin ‘yan bangan da gwamnati tasan da su na garin, Bunu Bukar ya ce sama da sojoji biyar sun mutu a wannan artabu.

“Ma’aikatan mu da harin ya ritsa da su sun ce Boko Haram sun kashe sojoji biyar sannan sun kwace motocin sojoji guda 7 sun tafi da su.

Jami’in yada labarai na rundunar John Enenche ya ce maharan sun far wa garin Kukawa ne domin Kora mutanen da suka Fara dawowa garin daga sansanin ‘yan gudun hijira.

Enenche ya ce sojoji 3 sun mutu sannan biyu sun ji rauni a jikin su a harin.

Ya ce sojojin da suka ji rauni na asibiti ana duba su.

Boko Haram A Kukawa

Majiya ta ce farmakin da ake cewa an kai a Kukawa, ya zo daidai lokacin da aka kai na Magumeri.

Kukawa na karkashin Baga inda aka kai wa Gwamna Babagana Zulum Hari makonni uku da suka gabata.

Majiyar cikin jami’an tsaro ta ce tabbas an kai mummunan hari a garin Kukawa, amma duk wani bayani bayan wannan, ji-ta-ji-ta ce, ba a tabbatar ba da abin da ya faru bayan nan.

“Mun san an kashe mutane da yawa. Amma ba mu da cikakken bayani. Maganar cewa Boko Haram sun kwace garin, har sun kafa tuta, ji-ta-ji-ta ce, ba mu tabbatar ba.” Inji majiyar.

Amma kuma Sahara Reporters da Daily Trust sun buga labarin cewa Boko Haram sun kama garin Kukawa, kuma sun yi garkuwa da mutane daruruwa.

Trust ta ruwaito Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce Boko Haram sun kama garin Kukawa ranar Talata da dare, bayan al’ummar garin sun koma da zama garin.

Mazauna Kukawa sun shafe shekaru biyu su na zaman gudun hijira a sansani. Boko Haram sun mamaye garin bayan mutanen garin sun koma da zama, ba da dadewa ba.

Share.

game da Author