Shin da gaske ne gwamnati za ta rabawa ‘yan Najeriya naira 30,000 tallafin rage radadin Korona? – Bincike Dubawa

0

Kafafen sada zumunta da wasu shafuka a yanar gizo sun zamo wurare da ake yada labaran karya da kuma kirkiro hanyoyin yin damfara ga mutanen da basu ji ba basu gani ba tun bayan barkewar annobar Korona a duniya.

A irin haka ne aka rika yadawa cewa wai gwamnatin Najeriya zata rabawa ‘yan Kasa naira 30,000 ga kowannen su a matsayin tallafin rage radadin Korona.

Wannan shafi da aka buga wannan magana a ya kun shi har da sakon karya da aka wallafa wai daga mai ba shugaban kasa shawara ne kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fito, wai yana horon mutane su je su cika Fom don samun tallafin naira 30,000.

Dubawa ta yi muku binciken kwa-kwaf da kuma bankano ainihin gaskiyar wannan magana, haka ne ko ba haka ba?

GASKIYAR MAGANA: Gwamnatin Najeriya ba ta sanar cewa zata rabawa ‘yan kasa naira 30,000 a matsayin kudaden tallafin rage radadin Korona ba. Sannan kuma Hukumar (NITDA) ita ma ta karyata wannan sanarwa cewa babu wani abu mai kama da haka da gwamnatin Najeriya ta shirya.

Cikakken Bayani

Kafafen sada zumunta dake a yanar gizon ne aka fi yada irin wadannan bayanan karerayi. A kan cewa gwamnati za ta raba naira 30,000 kuwa har an saka cewa sai an cika wani fom sannan za a iya samun damar cancantar samun wadannan kudade. Har suna rika saka wa a wadannan shafuka cewa za a raba ‘ Kudin tallafin rage radadin Korona a dalilin zaman kulle da aka sa mutane su yi a gidajen su’ sannan mun gano an bude wannan shafi a yanar gizo ne ranar 15 ga Yuni, 2020 kuma har ya samu mabiya da dama.

A Maris, aka fitar da sako cewa mai ba shugaba Buhari Shawara Kan Karkokin Yada Labarai, Femi Adeshina, ya tabbatar cewa lallai gwamnatin tarayya zata rabawa duk wadanda ke da mallakin shaidar asusun ajiya a banki wato BVN, ya garzayo za a bashi wannan tallafi.

A dalilin ganin irin wannan rudani da hakan ya haifarwa, Dubawa ta fantsama domin bin diddigin maganganun sannan da fede biri daga kai har wutsiya kowa ya gane gaskiya abin.

Bincike da aka Gundanar

Tun farko dai Dubawa ta fara ne da dira shafin Hukumar Kula da Harkokin Fasaha, a nan karara hukumar ta karyata wannan batu na raba kudade, tace wannan magana ba gaskiya bane, ta kuma gargadi ‘yan Najeriya da su nisanta kan su daga fadawa tarkon irin wadannan mutane dake amfani da shafukan yanar gizo domin damfarar mutane.

Ita ma Ma’aikatar bada Agaji da cigaban Al’umma ta fito ta karyata wannan maganan rabon kudi sannan ta gargadi mutane da su kaffa-kaffa da fadawa tarkon irin mutane haka dake yada irin wadannan sakonni.

Bayan haka, karin bincike da muka gudanar da taimakon na’uran Scam Doc (na’uran da ke gwada ingancin shafukan yanar gizo) ya nuna rashin sahihancin wannan shafi na yanar gizo da aka yada wannan maganar rabon kudi, gwajin ya ba shafin kashi 1% ne tak.

Sannan kuma an gano cewa irin wa dannan shafuka na yanar gizo masu leke da kwasar sirrin mutane ne; kaman bayanan su na banki domin su yi amfani da su wajen sata ko kulla makirci akan wanda ya fada tarkon.

Abinda muka Gano

Bisa ga bincike da nazarin da muka yi, mun tabbatar da cewa wannan shafi na yanar gizo da ya kago wannan magana ya kantara karya ne babu magana irin haka ko kuma mai kama da haka da gwamnatin Najeriya ta yi ko ta ambata ta hanyar wani. Gaba daya dai wannan labari KARYA ne, mutane a yi hattara dai.

Share.

game da Author