Wasu ‘yan iskan gari sun daka warsoson makudan kudaden da ‘yan fashi suka sato daga Bankin First Bank da ke garin Okeho, cikin Karamar Hukumar Kajola ta Jihar Oyo.
Basaraken garin, Onjo ns Okelo, Rafiu Mustapha, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan iskan gari ne suka daka wa kudaden wasoso, bayan da ‘yan kato-da-gora da maharba suka tare ‘yan fashin, har aka kama hudu daga cikin su.
Ya ce ana nan ana binciken gano wadanda suka gudu da kudaden, domin su dandana kudar hukuncin abin da suka aikata.
Wani jami’in bankin da ba ya so a bayyana sunan sa, ya shaida wa wakilin mu cewa maharba da ‘yan bijilante da mutanen arziki suka tare motar da barayin ke ciki bayan sun sato kudin.
“Sun tare motar, suka hana su wucewa, har ta fadi. Daga nan suka yi nasarar damke ‘yan fashi hudu kuma suka rarrafke su nan take.
“Yan fashi sun ciko buhunan shinkafa da kudi naira milyan 60. Amma yayin da aka tare motar, sai wasu ‘yan iskan gari suka bankara motar da karfi, suka kekketa buhunan kudin suka daka wasoson kudin kakaf.
“Duk wani kokarin da mutanen garin suka yi da suka kama ‘yan fashin, ya tafi a banza kenan. Domin matasa maza da mata sun biyo bayan an kama barayin, sun daka wasoson kudin karkaf.
“To mene ne bambancin ‘yan fashin da kuma ‘yan iskan gari wadanda suka kwace suka daka wasoso? Babu bambanci ai! Inji shi.
Ya ce kudin sun kai naira milyan 60, kuma har yau ko sisi ba a karbo hannun kowanen su ba.
Manajan Shiyya na First Bank a garin, Saheed Aiyelagbe, ya ce ba zai iya shaida fuskokin wadanda suka sace kudin ba.
“Saboda ‘yan fashin sun tilasta mun kwanta. Ba kuma zan ce maka ga adadin kudaden ba, domin mu mu na cikin banki a kwankwance.”
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya ce an kama wasu da ake zargi. Sannan kuma an sake kamo wasu uku an hada.
Ya ce da an samu cikakken bayanan kammala bincike, zai sanar da manema labarai abin da aka binciko.