Sarkin Gombe ya nada sabon Bargan Gombe

0

Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya daga likkafar Ciroman Zagin Gombe, Alhaji Abubakar Muhammad Gidado zuwa matsayin Bargan Gombe.

Alhaji Abubakar Gidado, shi ne mutum na farko a tarihin Masarautar Gombe da aka taba nadawa wannan mukami wanda yake da tarihi a daular Usumaniyya.

Da yake zantawa da wakilin mu, Alhaji Abubakar Gidado ya nuna farin cikin sa kan wannan sarauta ta Bargan Gombe.

A cewar Alhaji Abubakar Gidado, sarautar Barga sai wanda Sarki ya yarda da shi yake kusa da shi sosai sannan ake bai wa sarautar saboda mukami ne na babban hadimin Sarki akan kowanne aiki.

Barga kuma shi ne mai kula da dawakan sarki da sirdin sarki da kuma irin kayan da sarki zai sa idan zai yi hawa kaga dole sai amintaccen sarki ba wanda za’a iya hada kai dashi a cutar da mai martaba ba.

Alhaji Abubakar Gidado, bayan amintaccen Sarki ne kuma dan boko ne wanda yayi karatun digiri din sa na farko da na biyu a kasar Indiya yanzu ya dawo Najeriya yana digiri din sa na uku wanda saura masa shekara daya ya kammala.

Ya kara da cewa tunda ya zama amintaccen Sarki har aka nada shi wannan matsayi in sha Allahu yace ba zai ci amanar Sarki ba kuma ba zai ba shi kunya ba.

Bargan na Gombe ya yi amfani da wannan damar ya godewa majalisar sarki bisa kyawawan shawarwari da suke bai wa Sarkin suke kuma taya shi zakulo mutanen da suka dace ake nada su sarautun da suka cancanta.

Alhaji Abubakar Gidado ya yi alkawari ci gaba da yiwa mai martaba hidima kamar yadda ya saba.

Share.

game da Author