Sama da yara biliyan 1 Korona ta gurgunta karatun su – Majalisar Dinkin Duniya

0

Shugaban majalisar dinkin duniya UN Antonio Guterres ya koka kan yadda annobar Korona ta gurgunta karatun yara a fadin duniya.

Guterres bayyana haka a wani zaman majalisar da a akyi ranar talata.

Ya ce annobar Korona ya gurgunta yanayin karatun yaran duniya da ba a taba ganin irin sa ba.

Guterres ya ce kafin bayyanan Korona yara sama da miliyan 250 basu zuwa makaranta a fadin duniya. A dalilin wannan cuta ta Korona sai yawan yaran ya karu don ko ya zarce mutum biliyan 1.

Ya Kuma ce amfani da yanar gizo da sauran na’urorin fasaha da ake yi domin ilimantar da yara yayi matukar tasiri sosai sai dai kuma yaran talakawa da kasashen da basu da cigaba irin na yanar gizo, wadanda ke sansanonin ‘yan gudun hijira, da nakasassu duk sun fada cikin matsalar rashin samun ilmi.

Ya ce a dalilin haka wadannan yara sun fantsama cikin matsalolin da ya hada da yi wa yara auren wuri, rashin cin abincin dake karfafa garkuwa jiki, rashin daidaita jinsin Masa da Mata da dai sauran su.

Guterres ya bayyana wasu hanyoyi hudu da za su taimaka wajen farfado da fannin ilimi a wannan lokaci da ake fama da annobar Korona a Duniya.

Wadannan hanyoyi sun hada da bude makarantu, Kara ware wa fannin ilimi kudade, Kai wa yaran dake kauyuka ilimin boko sannan da amfani da dabarun koyarwa na zamani a kauyuka domin yaran dake karkara su amfana.

Share.

game da Author